logo

HAUSA

Gwamnatin Nijar ta yi nasarar dakile yunkurin juyin mulki

2021-04-01 09:39:23 CRI

Mai magana da yawun gwamnatin Jamhuriyar Nijar Zakaria Abdourahaman, ya bayyana cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai jiya da rana cewa, yunkurin juyin mulkin da wasu suka yi kokarin shiryawa da asubahin ranar Laraba a Niamey, babban birnin kasar bai yi nasara ba.

Abdourahaman ya bayyana cewa, an riga an kama mutane da dama dake da hannu a yunkurin juyin mulkin, ana kuma farautar wasu. An kuma fara gudanar da bincike, don gano tare da damke wadanda suka kitsa juyin mulkin da masu goya musu baya

Ya ce, a madadin gwamnati, yana ba da tabbacin cewa, al’amura sun dawo dai-dai, don haka, jama’a su ci gaba da gudanar da harkokinsu na rayuwa kamar yadda suka saba. Sai dai jami’in bai bayyana wadanda suka mutu a yunkurin juyin mulkin ko dalilin kitsa shi ba.

Tun da misalin karfe 3 na daren ranar Laraba agogon kasar ta Jamhuriyar Nijar ne, aka rika jin karar manyan bindigogi a kusa da fadar shugaban kasar dake Niamey. A cewar mazauna dake kusa da lamarin ya faru, an shafe kimanin mintuna 30 ana musayar wuta.

Yunkurin juyin mulkin dai na zuwa ne, kwanaki biyu kafin shugaban kasar da aka zaba Mohammed Bazoum, ya karbi ragama daga shugaban kasar mai barin gado Mahamadou Issoufu, wanda ya yi wa’adin mulki biyu a kasar ta Nijar.(Ibrahim)