logo

HAUSA

Jami’in Nijar ya yabawa kamfanin Sin bisa kaimi da ya sanyawa kasarsa wajen samun bunkasuwa mai dorewa a sha’anin samar da man fetur

2021-07-29 12:58:27 CRI

Ministan harkokin man fetur da makamashi, da makamashi mai dorewa na jamhuriyar Nijar Mahamane Sani Mahamadou, ya ziyarci rijiyar hakar mai ta Agadem, inda Nijar da Sin suke yin hadin gwiwar hako danyen man fetur. Yayin ziyarar tasa, ministan ya bayyana cewa, an kafa sha’anin hakar man fetur a Nijar, da kuma samun bunkasuwa cikin sauri a cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, ta dogaro da fasahohin kamfanin kasar Sin, wadanda suka inganta karfin Nijar na samun bunkasuwa mai dorewa.

Mahamadou ya yabawa gudummawar da kamfanin samar da man fetur da iskar gas na kasar Sin wato CNPC ta bayar a jamhuriyar Nijar. Ya ce, baya ga biyan bukatun cikin gida na kasar Nijar, za a kuma fitar da man fetur zuwa kasashe makwabta.

A watan Yuni na shekarar 2008, kamfanin CNPC da gwamnatin kasar Nijar, sun daddale yarjejeniyar aikin hadin gwiwa a rijiyar hakar mai ta Agadem, ciki har da hakar man fetur, da yin jigilar man fetur ta bututu masu tsayi, da gina kamfanonin tace mai. (Zainab)