logo

HAUSA

‘Yan bindiga sun hallaka sojojin jamhuriyar Nijar 15

2021-08-02 19:56:45 CRI

‘Yan bindiga sun hallaka sojojin jamhuriyar Nijar 15_fororder_b21c8701a18b87d682b492287937ce301e30fddf

Ma’aikatar tsaron jamhuriyar Nijar ta tabbatar da rasuwar dakarun sojin kasar 15, da kuma wasu karin sojojin 6 da suka bace, sakamakon wani kwantan-bauna da wasu masu dauke da makamai suka yi musu a Torodi, dake yankin yammacin jihar Tillabery, kusa da kan iyakar kasar da Burkina Faso.

A cewar sanarwar, jim kadan bayan harin, ‘yan sanda da wani rukuni na sojojin kasar sun samu dauki daga sojojin sama, inda suka kaddamar da samame a yankin da lamarin ya auku.

A baya bayan nan yankin yammacin jamhuriyar Nijar na shan fama da hare haren masu dauke da makamai, wadanda ake dangantawa da kungiyoyin ‘yan ta’adda masu nasaba da Al Qa’ida a yankin Maghreb, irin su (Aqim), da Ancar Dine, da sauran mayaka masu sansani a arewacin kasar Mali.      (Saminu)