logo

HAUSA

An jiyo karar harbin bindiga a kusa da fadar shugaban janhuriyar Nijar

2021-03-31 20:03:29 CRI

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa, da misalin karfe 3 na asubahin yau Laraba, an ji karar harbe harben bindiga a kusa da fadar shugaban kasar. Mazauna yankin da fadar gwamnatin take sun ce an kwashe kimanin tsawon rabin sa’a ana jin harbe harben.

Baya ga wannan, an kuma ji wasu harbe harben da sanyin safiyar yau din, a kusa da filin jirgin saman birnin Yamai, inda sansanin sojojin kasar yake.

Yanzu haka dai dakarun dake tsaron fadar shugaban kasar, sun kafa shingaye a dukkanin muhimman hanyoyin dake zuwa fadar shugaban kasar.  (Saminu)