logo

HAUSA

Kasar Sin ta mutunta burin jama’ar Afghanistan da abin da suka zaba

2021-08-17 10:53:00 CRI

Kasar Sin ta mutunta burin jama’ar Afghanistan da abin da suka zaba_fororder_1127767525_16291628024121n

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang ya bayyana matsayin kasar Sin kan halin da ake ciki a kasar Afghanistan, a yayin taron da kwamitin sulhu na MDD ya gudanar cikin gaggawa a jiya, kan batun Afghanistan.

A yayin taron, Geng Shuang ya ce, an samu babban sauyi a Afghanistan. Kasar Sin ta mutunta burin jama’ar Afghanistan da abin da suka zaba. Aikin gaggawa da za a yi yanzu shi ne mayar da kwanciyar hankali, zaman lafiya, oda da tsari a wannan kasa cikin hanzari, tare da yin iyakacin kokarin hana jikkatar mutane da asarar rayuka, da kuma magance samun dimbin ‘yan gudun hijira. Haka kuma dole ne a kiyaye hakkokin hukumomin jakadanci da ma’aikatan diplomasiyya a Afghanistan, sa’an nan dole ne a girmama da kare tsaron al’ummun kasa da kasa a Afghanistan da kuma muradunsu. Dukkan sassan Afghanistan na da alhakin kare rayukan jama’ar kasar da kuma dukiyoyinsu, tare da ba da tabbaci ga yadda mutanen waje suke zaune a kasar da janyewarsu yadda ya kamata.

Wakilin kasar Sin ya kara da cewa, har kullum kasar Sin na tsayawa kan cewa, warware batun Afghanistan a siyasance, ita ce hanya daya kacal da za a bi. Ya ce Sin na fatan kungiyar Taliban da jam’iyyu da kabilu a Afghanistan za su hada kansu wajen kafa wani tsarin siyasa, wanda zai dace da halin da wannan kasa take ciki, kuma zai bude kofa ga kowa, a kokarin aza harsashi kan samun dauwamammen zaman lafiya a kasar.

Geng ya ci gaba da cewa, kasar Sin na fatan kungiyar Taliban za ta cika alkawarinta na katse hulda tsakaninta da dukkan kungiyoyin ta’addanci. Kamata ya yi kasashen duniya su sauke nauyin da ke bisa wuyansu bisa dokokin kasa da kasa da kudurorin kwamitin sulhu, su hada kai wajen yaki da ta’addanci, su tsaya haikan wajen hana karuwar mambobin kungiyoyin ta’addanci na IS, da al-Qaeda da East Turkestan Islamic Movement. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan