logo

HAUSA

Me ya sa sojojin gwamnatin Afghanistan suka sha kaye? Kuma yaya makomar kasar a nan gaba?

2021-08-16 14:36:36 cri

Me ya sa sojojin gwamnatin Afghanistan suka sha kaye? Kuma yaya makomar kasar a nan gaba?_fororder_微信图片_20210816135040

A ranar 15 ga wata bisa agogon wurin, yanayin siyasa a Afghanistan ya canza ba zato ba tsammani, shugaban kasar Ashraf Ghani ya bar kasar. A wannan rana kuma, kungiyar Taliban a Afganistan ta fitar da sanarwa ta kafafen sada zumunta, inda ta amincewa dakaru masu dauke da makamai su shiga Kabul. A halin yanzu, Taliban ta riga ta kwace iko da fadar shugaban kasar. A cikin kwana guda, yanayin siyasa a Afghanistan yayi matukar sauyawa, wanda ya zarce yadda ake tsammani.

A ranar 11 ga watan Agusta, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya taba ruwaito nazarin hukumomin leken asirin Amurka yana cewa, mai yiwuwa kungiyar Taliban zata yi wa Kabul kawanya cikin kwanaki 30, kuma za ta mamaye birnin cikin kwanaki 90. Amma a hakika, a cikin kwanaki hudu da suka gabata, kungiyar Taliban ta kammala ayyukanta na shiga Kabul har da mamaye fadar shugaban kasar.

Sojojin gwamnatin Afghanistan sun yi ikirarin cewa sun zarce mutane dubu 300. Ba wai kawai an wadata su da kayan aiki na Amurka ba ne, har ila yau suna samun horo daga Amurka a duk shekara. Bisa halin da ake ciki, ko da ba su da wata fa'ida a fagen daga, ba za su kai wani mumunan matsayi ba. Amma abin da muke gani shi ne, a mafi yawan lokuta a maimakon sojojin gwamnatin Afghanistan sun yi jayayya ba, sai sun mika wuya kai tsaye.

Manazarta na ganin cewa, hasarar da sojojin gwamnatin Afganistan suka samu a fagen daga ya samo asali ne daga yaduwar cin hanci da rashawa a rundunar soji da janyewar sojojin Amurka daga kasar.

Gwamnatin Amurka ta fitar da rahotanni da dama a cikin ‘yan shekarun nan da ke nuna cewa, sojojin Afghanistan suna da matsalar cin hanci da rashawa da aka dade ana fama da ita. Manyan hafsoshin soja sun ajiye kudaden da aka ware wa sojoji a aljihunsu, har ma sun sayar da makamai ta haramtacciyar kasuwa don amfanin kansu. Bugu da kari, rundunar sojojin gwamnatin Afganistan su kan bayar da rahoton karya game da yawan sojojin da suke da su don karbar karin kudaden soji.

Me ya sa sojojin gwamnatin Afghanistan suka sha kaye? Kuma yaya makomar kasar a nan gaba?_fororder_微信图片_20210816135103

NATO, wanda Amurka ke jagoranta, ta kiyaye tasirin da take dashi kan kungiyar Taliban, amma sannu a hankali bayan janyewar dakarun Amurka da na NATO, Taliban ta dena fargaba wajen fadada ikonta a kasar.

A hakikanin gaskiya, Amurka ba za ta iya yin watsi da laifinta kan hasarar da sojojin gwamnatin Afganistan suka yi da tabarbarewar halin da ake ciki a kasar ba. A shekaru ashirin da suka gabata, Amurka ta kaddamar da yaki don murkushe mayakan Taliban tare da haddasa rarrabuwar kan al'ummar kasar Afghanistan. A cikin shekaru 20 da suka gabata, Amurka ta tilasta kyautata tsarin siyasa da na zamantakewa na Afghanistan, wanda ya haifar da sakamako marar kyau saboda rashin dacewa. Ga shi yanzu, janyewar Amurka ta sanya kasar Afghanistan ta koma yadda take a baya.

Manazarta a fannin harkokin siyasa a Afghanistan gaba daya sun yi tsamanin cewa, duk da cewa ‘yan Taliban sun mallaki mafi yawan yankunan kasar, amma tun da Afghanistan kasa ce mai kabilu da addinai daban-daban, kuma al’adun yammacin duniya na yin tasiri sosai ga manyan biranen kasar, ciki har da Kabul, don haka, ya yiwu za a kara samun sauye-sauyen yanayin da ake ciki a kasar a gaba.

A cewar rahotannin kafofin yada labarai, duk da cewa Amurka ta janye jikinta daga Afghanistan, amma har yanzu tana kiyaye babban tsarin leken asiri a kasar, akwai yiyuwar za ta sake ba da goyon baya ga mayaka masu adawa da kungiyar Taliban.

Kasashen duniya suna ganin cewa, batun na Afghanistan yana bukatar bangarorin da abin ya shafa su cimma shirin sulhu na siyasa a teburin tattaunawa. Amma, saboda yadda Taliban ta sami babbar nasarar a aikin sojin da ta gudanar, don haka, watakila ba za ta dora muhimmanci kan shawarwarin Doha da ke gudana ba. Sabili da haka, wasu sun yi imanin cewa, nan gaba Afghanistan na iya sake fadawa cikin mawuyacin hali na yakin basasa bayan da Taliban ta karbi mulkin kasar a dukkan fannoni. (Mai fassara: Bilkisu)