logo

HAUSA

Hua Chunying: Sin na martaba zabin al’ummar Afghanistan

2021-08-16 19:09:39 CRI

Hua Chunying: Sin na martaba zabin al’ummar Afghanistan_fororder_华春莹

Da yammacin yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta ce a yanzu haka Afghanistan na fuskantar wasu manyan sauye sauye, kuma Sin na martaba zabin da al’ummun kasar suka yiwa kan su.

Hua, wadda ta jagoranci taron manema labarai na yau, ta ce Afghanistan ta fuskanci tashe tashe na tsawon sama da shekaru 40. Don haka kawo karshen yaki a kasar bukata ce ta al’ummar Afghanistan, kuma buri ne na bai daya na sassan kasa da kasa, kana fata ne na kasashen dake yakin ta.

Hua ta ce tsagin Sin ya lura da ikirarin kungiyar Taliban, cewa an kawo karshen yakin da ake gwabzawa, kuma tana shirye shiryen kafa budaddiya kuma cikakkiyar gwamnatin Islama, kana za su aiwatar da matakan tabbatar da tsaron rayukan al’ummun Afghanistan, da ma baki da masu aikin diflomasiyya dake kasar.

Hua Chunying ta jaddada cewa, Sin na fatan Taliban din za ta aiwatar da wannan matakai, domin cimma nasarar kafa gwamnati cikin lumana. Yayin da aka gabatar da tambaya game da ko Sin za ta amince da jagorancin kungiyar Taliban? Hua Chunying ta ce Sin na martaba ikon al’ummun Afghanistan, ta yadda za su kai ga cimma burikan su, da makomar da suka sa a gaba. Kaza lika Sin na fatan ganin Taliban ta kafa tsarin siyasa da zai game dukkanin sassa, da kabilun kasar, domin kaiwa ga yanayi na wanzar da zaman lafiya da lumana a kasar. (Saminu)