Warware batun Afghanistan a siyasance, hanya ce daya tilo da za a bi wajen samun zaman lafiya a kasar
2021-08-14 17:07:48 CRI
An rufe taron kwanaki 3 da aka yi tsakanin sassa daban daban kan aikin shimfida zaman lafiya a kasar Afghanistan a birnin Doha, hedkwatar kasar Qatar a daren ranar 12 ga wata, inda wakilai daga kasashen Sin, Rasha, Pakistan, Amurka da wasu kungiyoyin kasa da kasa suka halarta.
Taron ya kalubalanci gwamnatin Afghanistan da kungiyar Taliban da su dauki matakai don samun aminci a tsakaninsu, a kokarin samun sulhu a siyasance da tsagaita bude wuta daga dukkan fannoni cikin hanzari.
Yue Xiaoyong, wakilin musamman na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin wanda ke kula da batun Afghanistan ya zanta da manema labaru bayan taron, inda ya ce, dukkan mahalarta taron suna ganin cewa, karfin soja ba zai iya warware batun Afghanistan ba. Warware batun a siyasance ta hanyar shawarwari, ita ce hanya daya tilo da za a iya bi wajen samun dawamammen zaman lafiya a kasar ta Afghanistan.
Wakilin musamman din ya yi nuni da cewa, a matsayinta na kasar da ke makwabtaka da Afghanistan, kasar Sin za ta ci gaba da kara azama kan aikin shimfida zaman lafiya a kasar, tare da hada kai da kasashen duniya da ma sauran kasashen da ke makwabtaka da Afghanistan wajen lalubo hanyar samun sulhu da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban kasar cikin hanzari. (Tasallah Yuan)
Labarai Masu Nasaba
- Ministan tsaron Birtaniya: Janyewa daga Afghanistan da sojojin Amurka suka yi, kuskure ne
- An yi taron ganawar wakilan kasashen Sin da Amurka da Rasha da Pakistan kan batun Afghanistan
- Ministan wajen Pakistan ya soki lamirin ficewar dakarun Amurka da NATO daga Afghanistan
- Pentagon: Amurka za ta ci gaba da tallafawa dakarun Afghanistan a yakin da suke yi da kungiyar Taliban