Mayakan Taliban sun kama birnin Jalalabad dake gabashin Afghanistan
2021-08-15 16:38:55 CMG
Mai magana da yawun mayakan Taliban Zabihullah Mujahid, ya bayyana cewa, da safiyar yau mayakan kungiyar sun kame galibin muhimman sassan birnin Jalalabad dake gabashin kasar Afghanistan. Kakakin kungiyar ya yi wannan ikirarin ne a shafinsa na sada zumunta, inda ya bayyana cewa, mayakan sun kame galibin sassan birnin na Jalalabad, babban birnin lardin Nangarhar, kimanin kilomita 120 gabas da Kabul, babban birnin kasar.
Ya bayyana cewa, mayakan na Taliban, suna kokarin kwace iko da ofishin gwamna da hedkwatocin ‘yan sandan lardin dake Jalalabad. A ranar Asabar ne dai, suka kwace lardin Kunar, tare kuma da ayyana cewa, sun kwace biranen Mazar-i-Sharif da Maimana, dake yankin arewaci, sai kuma biranen Gardez da Mehtarlam dake gabashin kasar.
Sai dai gwamnatin Afghanistan ba ta tabbatar da ikirarin na Taliban ba tukuna.(Ibrahim)