logo

HAUSA

Yadda kasashen yamma ke yaudarar ‘yan Najeriya da bayanai marasa gaskiya

2021-08-15 18:43:11 CMG

Yadda kasashen yamma ke yaudarar ‘yan Najeriya da bayanai marasa gaskiya_fororder_0815-sharhi-COVID-19-Bello

Jaridiar The Guardian ta kasar Najeriya ta wallafa wani labari mai taken “Kasar Sin ta ki amincewa da bukatar WHO ta ci gaba da gudanar da bincike kan asalin cutar COVID-19” a ranar Juma’ar da ta gabata. Wannan labarin da jaridar da samo daga kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa AFP ya sabawa ainihin bayanin da aka bayar a wani taro, da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira a ranar Juma’a, tare da neman dora wa kasar Sin laifi na “hana gudanar da aikin binciken gano asalin kwayar cuta”.

Wannan labarin da kamfanin AFP ya gabatar ya ce, kasar Sin ba ta so a gudanar da aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19, amma a hakika, Ma Zhaoxu, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana a taron na ranar Juma’a cewa, kasar Sin har kullum tana goyon bayan aikin binciken gano asalin cutar ta hanyar kimiya da fasaha, kana za a ci gaba da aikin. Ban da wannan kuma, kasar ta riga ta mika wani cikakken shirin aiki ga hukumar lafiya ta duniya WHO. Abin da kasar Sin ta bayyana shi ne, tana adawa da yunkurin siyasantar da batun aikin binciken gano asalin kwayar cutar.

Kana labarin AFP ya sabawa muhimmiyar ka’idar rubuta labarai, wato duk wani bayanin da aka bayar, ya kamata a bayyana wurin da aka samu bayanin, inda ya ce rahoton da WHO da kasar Sin suka bayar bayan gudanar da bincike a birnin Wuhan a farkon bana, wai rahoto ne “na siyasa”. Kana ya ce wai wasu kwararru, ko da yake ba a bayyana sunan ko daya daga cikinsu ba, na kara yarda da tunanin yiwuwar bullar kwayar cutar COVID-19 daga dakin gwaji.

Hakika a yayin taron da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira a ranar Juma’a, an riga an bayyana hakikanan abubuwan da suka abku da ra’ayin kasar Sin dalla-dalla, sai dai sam ba a nuna su ba a cikin rahoton kamfanin AFP. Hukumar WHO da kasar Sin sun gudanar da wani bincike game da asalin cutar COVID-19 a birnin Wuhan na kasar Sin tare, inda suka kammala wannan bincike tare da gabatar da wani rahoto, wanda ya riga ya samu amincewa daga gamayyar kasa da kasa, don haka bai kamata ba a yi watsi da rahoton ba gaira ba dalili, sa’an nan kuma a sake gudanar da wani bincike a birnin Wuhan. Ban da wannan kuma, bukatar sake gudanar da bincike a Wuhan wata bukata ce da sakatariyar hukumar WHO ta gabatar, kuma hakan keta ka’idojin hukumar ce, domin ta gabatar da bukatar bisa radin kanta, ba tare da tattaunawa da mambobin hukumar ba, balle ma samun amincewa daga wajensu. Kana a nata bangare, kasar Sin ta san ba a taba samun wata matsala a cibiyar nazarin kwayoyin cuta ta Wuhan ba, kana cikin ma’aikatan cibiyar ba wanda ya kamu da cutar COVID-19. Wato idan ana son gudanar da bincike ta hanyar kimiya da fasaha, to, babu bukatar gudanar da shi a cibiyar dake Wuhan, sa’an nan idan binciken ya kunshi burin siyasa, to, tabbas ne za a dora wa kasar Sin laifi. Ban da wannan kuma, tun bayan barkewar annobar COVID-19, masana na kasar Sin sun yi ta kokarin hadin gwiwa tare da takwarorinsu na sauran kasashe, don gudanar da bincike game da asalin cutar COVID-19, inda suka riga suka gabatar da kundaye fiye da 600, da raba bayanai game da kwayar cutar COVID-19 ga kasashe daban daban. Hakan ya nuna cewa, har kullum ana kokarin gudanar da aikin bincike game da gano asalin kwayar cutar, ba tare da wata rufa-rufa ba, kuma ba a taba hana gudanar da binciken, ko kuma neman boye wasu abubuwa ba.

Sai dai labarin da kamfanin AFP ya wallafa a jaridar The Guardian, bai bayyana wadannan abubuwa ba, sannan bai ambaci sauran wasu bayanai masu alaka da wannan ci gaba ba. Misali, yadda aka dinga samun labaran kamuwar wasu mutane a kasar Amurka da kasashen Turai da cutar COVID-19 kafin barkewar cutar a Wuhan, da hadarin da ya abku a cibiyar gwajin kwayoyin cuta ta Fort Detrick ta kasar Amurka, da alakarsa da mutanen da suka kamu da cutar huhu da suke zama a kusa da cibiyar, da dai sauransu, dukkan wadannan abubuwa sun sa ake ganin cewa, idan ba domin wani burin siyasa na boye ba, me ya hana a gudanar da aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19 a kasar Amurka, ko kuma a wata kasa dake nahiyar Turai, maimakon sake gudanar da wani bincike a birnin Wuhan na kasar Sin?

Ban da wannan kuma, yadda ake samun tsamin dangantaka tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, da yadda kasar Amurka ke kokarin dora wa kasar Sin laifi sakamakon gazawar Amurka wajen hana yaduwar cutar COVID-19 a cikin gidanta, da yadda kasar Amurka ke matsawa hukumar WHO lamba,  duk wadannan abubuwa sun sa kasar Sin kasa kwantar da hankalinta da ba da damar sake gudanar da wani bincike a Wuhan, saboda matsin lamba na siyasa da kasar Amurka ke yi, ya riga ya gurgunta duk wani matakin kimiya da fasaha.

Ganin yadda kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya sun dade suna kokarin yada jita-jita game da kasar Sin, ya sa wannan labarin da kamfanin AFP ya tsara bai ba  ni mamaki ba ko kadan. Abin bakin ciki shi ne yadda aka wallafa wannan labari a shafin yanar gizo na jaridar The Guardian ta kasar Najeriya, domin za a iya amfani da wannan labari na jabu wajen yaudarar jama’ar Najeirya. Kana wani abun damuwa shi ne, dukkan labarun duniya da jaridar The Guardian ta wallafa kamfanin AFP ne ya tsara su. Wato, a kalla dai a fannin bayanan da suka shafi kasar Sin, jaridar The Guardian ta mai da idanu da kwakwalwar ‘yan Najeriya tamkar kwandon shara da za a jefa labarai na jabu da kafofin yada labarai na kasasahen yamma suka wallafa

Wannan batun ya sa na tuna da cewa, a watan Afrilun bara, wani lauya dan Najeriya ya bukaci gwamnatin kasar, da ta kai kara ga kotun kasa da kasa bisa zargin kasar Sin da “yada cutar COVID-19 a duniya” tare da neman a biya ta diyya. Wannan batu ya bakanta ran jama’ar kasar Sin sosai, domin har kullum kasar Sin tana kallon kasashen Afirka, ciki har da Najeriya, a matsayin abokanta. Kana kasar Sin ta ba da tallafin kayayyakin kandagarkin cuta karo 2 ga Najeriya, daidai kafin abkuwar lamarin. Yanzu idan mun sake duba wannan batu, muna iya cewa, ya yiwu an yaudari wannan lauya da wasu bayanai marasa gaskiya da kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suka watsa, ta yadda zai yarda da ma yin magana a madadinsu.

A nan ina so in yi kira ga jama’ar kasar Najeriya, da su dinga lura da wanda ya rubuta wasu labarai masu alaka da kasar Sin. Idan an samu labaran daga wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya ne, to, ya kamata a sake tantance su, sannan a kwatanta da labaran da kafofin yada labarai na kasar Sin suka samar, don kaucewa fadawa cikin tarkon da kasashen yamma suka dana, tare da burinsu na bata huldar dake tsakanin mutanen Najeriya da na kasar Sin. Gyara kayanka bai zama sauke mu raba ba.(Bello Wang)

Bello