logo

HAUSA

Ya Kamata Duniya Ta San Ainihin Halayyar Amurka

2021-03-20 18:01:53 CRI

Ya Kamata Duniya Ta San Ainihin Halayyar Amurka_fororder_203daf29f19b4282899a2e8595ce6d94

Taron farko na manyan jami’an Sin da Amurka da aka yi a Alaska, bai dakatar da illata dangantakar Sin da Amurka ba, kamar dai yadda wasu kafafen yada labarai suka yi hasashe, inda bangarorin biyu suka yi musayar yawu a kan ra’ayoyinsu.

Laifin lalata dangantakar bangarorin biyu na kan Amurka, domin yayin da aka zauna tattaunawar, Amurka ba ta nuna halin dattako a matsayinta na babbar kasa ba.

Yayin da suke musayar yawu, kasar Sin ta bayyana tsohon labari dangane da Amurka domin ba duniya damar ganin ainihin yadda kasar take.

Amurka na nuna iko, kuma ba ta da dabaru ko ka’idojin mulki. Da take tunkarar Sin da ta shirya tattaunawar da kyakkyawar niyya da kuma tsarukan da bangarorin biyu suka amince da su, Amurka ta zarce lokacin da aka kayyade na bude taron, tare da farawa da sukar Sin da zarge-zarge marasa tushe, kan manufofinta na gida da waje. Wannan bai dace da yanayin karban baki ba, kuma irin wannan cin zali ne Amurka ta dade tana yi.

Da yake mayar da martani, Yang Jiechi, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS kuma daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin tsakiyar, ya ce Taiwan da HK da Xinjiang, yankuna ne da ba za a iya raba su da kasar Sin ba, kuma Sin na adawa da Amurka ta tsoma baki cikin harkokinta na gida. Haka zalika, Amurka ba ta da ikon sukar kasar Sin a wannan fanni.

Ya Kamata Duniya Ta San Ainihin Halayyar Amurka_fororder_10b0518a0a734a28bf095c2669df3f8d

Amurka na da son kai kuma ba ta san ya kamata ba a matsayinta na babbar kasa. Kafin taron, sakataren harkokin wajen kasar, Anthony Blinken, ya ce akwai yuwuwar a tattauna batutuwan da suka shafi COVID-19 da sauyin yanayi da sauran wasu batutuwa. Amma da aka fara tattaunawar, Amurka ba ta dauki wadannan batutuwa a mastayin masu muhimmanci ga duniya ba, bare ma ta duba yuwuwar hada hannu da Sin.

Tawagar ta Biden na iya daukar abun da suka yi a Alaska a mastayin kare muradun cikin gida ko kawaye ko duniya, amma ba don warware matsala ba.

Sai dai, abun da duniya take gani shi ne, Amurkar da darajarta ta zube, kuma take cin zali kamar yadda ta saba. Duniya na ganin Amurka a matsayin mai iko da girman kai. Amurka kanta kawai ta sani, ba ta damu da sauran nauye-nauyen dake wuyanta ba. Abun da tawagar jami’an diflomasiyya ta Shugaba Biden dake son nisanta kansa da salon diflomasiyyar Trump suka yi, ya nunawa duniya abun da Amurka ta damu da shi.

Idan Amurka ta zabi mutunta juna da kauracewa rikici da fito-na-fito, ba makawa dangantakarta da Sin, za ta iya shawo kan matsaloli da samun ci gaba. Idan kuma rikici za a ci gaba da yi, to kasar Sin ta kware a wannan fage.

Fa’iza Mustapha