logo

HAUSA

Ya Zuwa Yanzu Gwamnatin Biden Tana Maimaita Kuskuren Fahimta Kan Kasar Sin

2021-04-29 21:05:24 CRI

Ya Zuwa Yanzu Gwamnatin Biden Tana Maimaita Kuskuren Fahimta Kan Kasar Sin_fororder_amurka

Ranar 28 ga wata, Shugaba Joe Biden na kasar Amurka, ya yi jawabi a majalisar dokokin kasarsa, yayin da yake cika kwanaki 100 da hawa kujerar mulkin kasar.

Dangane da huldar da ke tsakanin Amurka da kasar Sin, Biden ya zargi kasar Sin da laifin aiwatar da manufofin ciniki maras adalci. Ya kuma yi shelar cewa, Amurka za ta tabbatar da babban tasirinta ta fuskar aikin soja a yankin Indo Asia Pacific, tare kuma da kiyaye hakkin dan Adam da ‘yancin kai. A cikin kwanakin 100, Biden ya rika maimaita manufofin da tsohon shugaba Donald Trump ya aiwatar kan kasar Sin, har ma ya nuna alamu masu hadari a wasu fannoni.

Gwamnatin Biden ba ta nuna alamar sassauta yakin ciniki da Amurka ta tayar kan kasar Sin ba. Tana ci gaba da sanya wa kamfanonin kimiyya da fasaha na kasar Sin sabbin takunkumai. Kana kuma, gwamnatinsa ta rika illata moriyar kasar Sin dangane da batutuwan Xinjiang, Hong Kong, Taiwan da dai sauransu. Ban da haka kuma, Amurka ta yi ta yayata kalaman “kasar Sin ta fi kawo barazana”, tare da inganta tsarin tuntubar juna tsakaninta da kasashen Japan, India da Australiya. Ta kuma nemi samun goyon bayan kawayenta, da su yi atisayen soja da sintiri a kudancin tekun kasar Sin. Har ma ta yi shelar cewa, Amurka tana fuskantar babban hadari, saboda kasar Sin ta fi ta ci gaba, yayin da take ambaton farfado da ayyukan more rayuwar jama’a a Amurka, da raya sabbin makamashi.

Ko da yake an canza shugaban Amurka, amma gwamnatin Amurka ta rika yada zarge-zarge na wai kasar Sin tana kawo mata barazana. Tana yunkurin jefa duniya cikin wani sabon yakin cacar baka. Irin wannan kuskuren da ta yi kan manyan tsare-tsare, zai yi hadari sosai ga ita kanta da ma duniya baki daya.

Manufar kasar Sin ta raya kasa, ita ce kyautata kanta, da kuma taimakawa al’ummar kasar, ta yadda za su kara jin dadin zamansu, a maimakon kalubalantar wasu, ko kuma maye gurbin wasu. Aikin gaggawa da gwamnatin Amurka za ta yi a yanzu shi ne, dakatar da yunkurinta na kara yin fito-na-fito da kasar Sin, da komawa hanyar yin hadin gwiwa da Sin, da yin takara da Sin yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan