logo

HAUSA

Amurka na kokarin hada kai da wasu kasashe don matsawa kasar Sin lamba

2021-06-16 14:27:08 CRI

Amurka na kokarin hada kai da wasu kasashe don matsawa kasar Sin lamba_fororder___172.100.100.3_temp_6024_1_6024_1_1_39ed9170-1514-456e-849f-f2adbc1c8395

 

Ran 14 ga wata, an kira taron kolin kungiyar tsaro ta NATO, a hedkwatarta dake Brussels, fadar mulkin kasar Belgium. Bayan taron, a karon farko cikin wata hadaddiyar sanarwa, an bayyana cewa, kasar Sin ta haifar da kalubale a fannoni da dama.

Kafin wannan, a cikin sanarwa ta karshe da taron koli na G7, da aka rufe shi ba da dadewa ba a Cornwall na Birtaniya, an takali kasar Sin bisa batun kare hakkin Bil Adama, da Xinjiang, da Hong kong, da asalin cutar COVID-19 da dai sauransu.

Shugaban kasar Amurka Joseph Biden ya halarci wadannan taruka biyu, don neman kasashe mahalarta su zauna inuwa guda don yakar kasar Sin. Kafar yada labarai ta CNN ta ba da labarin cewa, Amurka na kokarin yin hakan, amma kasashen Turai ba su nuna sha’awar su sosai ba.

A karo na farko, shugaba Biden ya ziyarci Turai tun bayan ya hau kan mukamin shugabancin Amurka a watan Jarairun da ya gabata, kuma sau da dama ya sha bayyana aniyyarsa ta karfafa karfin kasarsa a tsakanin kasashen yamma. A wani bangare kuma, wani babban jami’in kasar Amurka ya bayyana cewa, kasarsa za ta shawarci taron kolin, da ya dauki matakai masu tsanani kan kasar Sin.

Kafar yada labarai ta AFP ta ba da labarin cewa, Biden na ci gaba da matakan Donald Trump na jagoranci G7, ta yadda za ta mai da hankali kan Beijing, don daukar matakai masu tsanani kan kasar Sin. A ganin kafar yada labarai ta AP, Biden zai dauki mataki iri daya kamar G7 a kan taron NATO, don kaiwa ga matsaya daya ta hadin kai don takalar kasar Sin.

A iya ganin cewa, wadannan taruruka biyu dukkansu na shafar kasar Sin, amma ba kamar yadda Amurka ta yi tsamani a baya ba, sauran kasashen yamma, musamman kasashen Turai ba su nuna sha’awa matuka kan takalar kasar Sin ba.

Jaridar “The Guardian” ta Birtaniya ta ruwaito maganar jami’an Amurka dake cewa, Biden na matukar fatan kasashe mambobin G7 za su zargi kasar Sin, kan batun tilasta yin aiki a yankin Xinjiang, a cikin hadaddiyar sanarwarta, amma sanarwar ba ta ambaci sunan kasar Sin kai tsaye ba.

Shafin yanar gizo na EU wato Eur Activ, ya ba da labarin cewa, Amurka tana son amfani da kalamai masu tsanani a cikin hadaddiyar sanarwar NATO, amma kasashen Turai sun yi amfani da kalmar kalubale a maimakon barazana.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya bayyana a gun taron manema labarai bayan taron kolin G7 cewa, G7 ba wata kungiya ce dake nuna kiyayya ga kasar Sin ba, maimakon haka G7 na son yin hadin kai da kasar Sin a fannin tinkarar sauyin yanayi, da cinikayyar duniya, da manufofin samun bunkasuwa da dai sauransu.

Ita ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel cewa ta yi, kasarta na da sabani da kasar Sin a wasu bangarori, amma suna da hadin kai a wasu bangarori na daban.

A nasa bangare, Firaministan kasar Italiya Mario Draghi na ganin cewa, kamata ya yi kasashen yamma sun yi hadin kai da kasar Sin a wasu manyan fannoni, musamman ma a fannin tinkarar sauyin yanayi.

Ita kuwa jaridar “Bild” ta Jamus cewa ta yi, ko da yake Amurka da Birtaniya da Canada, sun yi kira da a dauki matakai masu tsanani kan kasar Sin, amma Angela Merkel da Mario Draghi sun dakatar da su.

Abin lura shi ne, Amurka ta gabatar da “shawarar komawa duniya mafi kyau, wato B3W” kafin kaddamar da taron G7, da zummar taimakawa kasashe masu tasowa samar da manyan ababen more rayuwa da darajarsu za ta kai fiye da dala Amurka biliyan dubu 40, don yin takara da shawawar “Ziri daya da hanya daya” da Sin ta gabatar. Amma, jaridar “Financial Times” ta ba da labarin cewa, a karshe taron kolin G7, ba a cimma matsaya daya kan wannan shawarar da Amurka ta gabatar ba.

Matakan da Biden ya dauka bayan ya kama aiki na nuna cewa, Amurka na yunkurin zama inuwa guda da sauran kasashe, don kulla kungiya bisa ra’ayin siyasarsu wajen yaki da kasar Sin. Amma, abokanta a Turai ba su nuna sha’awa sosai ba. A hakika dai, taron koli na wannan karo ya nuna bambancin ra’ayi tsakanin kasashe mambobin G7, kungiyar ba ta dace da halin da ake ciki a yanzu ba.

Jaridar “Financial Times” ta Birtaniya ta ba da labarin cewa, ba kamar sauran shugabanni ba, shugabannin Turai sun nuna taka tsantsan kan batun kasar Sin. CNN ta ba da labarin cewa, Turai na nuna damuwa sosai kan matakan da Amurka ke dauka na takalar kasar Sin.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a jiya Talata cewa, abin dake shafar kasar Sin a cikin hadaddiyar sanarwar da G7 ta fitar, ya bayyana mummunan burin Amurka, da wasu karin kasashe na tayar da hankali, da habaka bambancin ra’ayi, kuma Sin na matukar nuna rashin jin dadinta kan hakan.

Kakakin tawagar Sin dake EU ya nuna cewa, sanarwar NATO cewa wai Sin ta haifar da kalubale a fannoni da dama karya ce game da bunkasuwar kasar Sin, kuma kuskure ne da ya shafi halin da ake ciki yanzu, wanda ya zama tunanin cacar baka, da neman cimma burin siyasa. (Amina Xu)