Pentagon: Amurka za ta ci gaba da tallafawa dakarun Afghanistan a yakin da suke yi da kungiyar Taliban
2021-08-10 10:44:31 CRI
Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce, rundunar sojojin kasar za ta ci gaba da tallafawa dakarun sojin Afghanistan, a yakin da suke yi da mayakan Taliban. Hakan na zuwa ne yayin da Taliban din ta kara kwace wasu yankunan kasar cikin karshen mako.
Da yake tsokaci kan hakan, sakataren watsa labaran Pentagon John Kirby, ya ce za su ci gaba da hada kai da mahukuntan Afghanistan a duk lokacin da suke da damar yin hakan, musamman ta hanyar kaddamar da hare hare ta sama.
To sai dai Mr. Kirby bai bayyana ko Amurka za ta dore da tallafin nata har bayan ranar 31 ga watan Agusta ba, wato lokacin da shugaba Joe Biden ya ayyana kammala ficewar sojojin Amurka daga Afghanistan.
An dai yi dauki ba dadi a biranen Afghanistan da dama, yayin da kuma kusan rabin lardunan kasar 34 suka fuskanci fito na fito, da musayar wuta a kan tituna tsakanin dakarun gwamnati da mayakan Taliban cikin makwannin baya bayan nan. (Saminu)