logo

HAUSA

Ministan wajen Pakistan ya soki lamirin ficewar dakarun Amurka da NATO daga Afghanistan

2021-08-10 11:07:22 CRI

Ministan wajen Pakistan ya soki lamirin ficewar dakarun Amurka da NATO daga Afghanistan_fororder_210810-Saminu4-Pakistan

Ministan ma’aikatar harkokin wajen Pakistan Mahmood Qureshi, ya soki lamirin ficewar dakarun Amurka da na kungiyar tsaro ta NATO daga Afghanistan, matakin da a cewarsa, zai baiwa dakarun Taliban damar cin karen su ba babbaka, tare da haifar da rashin kwanciyar hankali a kasar.

Mahmood Qureshi, ya ce Pakistan ta yi gagarumar sadaukarwa sakamakon tashe tashen hankula dake addabar Afghanistan, a hannu guda kasarsa na dandanar mummunan tasirin yakin da ke aukuwa a makwafciyarta.

Jami’in ya nuna damuwa, game da abun da ka je ya zo, yayin da dakarun Amurka da NATO ke janyewa daga Afghanistan. Ya ce dauki ba dadi a kasar ya haifar da kisan ’yan Pakistan 80,000, tare da asara mai yawa a fannin tattalin arziki.  (Saminu)