logo

HAUSA

Ministan tsaron Birtaniya: Janyewa daga Afghanistan da sojojin Amurka suka yi, kuskure ne

2021-08-14 17:03:10 CRI

Ministan tsaron kasar Birtaniya Ben Wallace, ya bayyana a jiya cewa, janyewa daga kasar Afghanistan da sojojin kasar Amurka suka yi, kuskure ne, wanda zai tsananta yanayin tsaro a kasar. Kuma akwai yiwuwar kasashen duniya su fuskanci hadari sakamakon hakan.

Wallace ya bayyana wa ‘yan jarida na kasar cewa, tun bayan da gwamnatin Amurka ta Donald Trump da kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan suka cimma yarjejeniyar janye sojoji daga kasar a farkon bara, ya ke ganin kudurin a matsayin kuskuren da zai haddasa kungiyar Al Qaeda ta dawo da ci gaba da tada zaune tsayen da ka iya kawo hadari ga sauran sassan duniya. Ya ce, idan yanayin tsaro ya tsananta a Afghanistan, to akwai yiwuwa sojojin Birtaniya za su koma kasar.

Ma’aikatar tsaron Amurka ta bayyana a jiya cewa, kungiyar Taliban tana yunkurin yi wa babban birnin kasar wato Kabul saniyar ware, sai dai Amurka ta damu da yanayin da kasar ke ciki. Kakakin ma’aikatar John Kirby ya bayyana cewa, Amurka za ta ci gaba da goyon bayan sojojin gwamnatin kasar Afghanistan, yana mai cewa sojojin na da karfin cimma nasara a yakin. (Zainab)