logo

HAUSA

An yi taron ganawar wakilan kasashen Sin da Amurka da Rasha da Pakistan kan batun Afghanistan

2021-08-12 10:50:44 CRI

An yi taron ganawar wakilan kasashen Sin da Amurka da Rasha da Pakistan kan batun Afghanistan_fororder_hoto

Jiya Laraba, an gudanar da taron ganawar wakilan kasashen Sin da Amurka da Rasha da Pakistan, kan batun kasar Afghanistan a birnin Doha, fadar mulkin kasar Qatar.

Wakilai daga kasashen hudu, sun tattauna kan yanayin da kasar Afghanistan take ciki, inda suka yi kira ga bangarorin da abin ya shafa, da su dakatar da yaki a tsakaninsu, su kuma kulla yarjejeniya kan wasu muhimman batutuwa.

Manzon musamman na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin dake kula da batun kasar Afghanistan Yue Xiaoyong, da wakilin musamman mai kula da harkokin kasar Afghanistan na gwamnatin kasar Amurka Zalmay Khalilzad, da wakilin musamman na shugaban kasar Rasha mai kula da batun kasar Afghanistan Zamir Kabulov, da kuma wakilin musamman na fitaministan kasar Pakistan dake kula da batun kasar Afghanistan Mohammad Sadiq sun halarci wannan taro.

Wakilan bangarorin hudu, sun cimma matsayi daya kan shimfida zaman lafiya a kasar Afghanistan ta hanyar yin shawarwari, da kuma kulla yarjejeniyar siyasa, inda suka yi kira da a girmama ’yancin kai da cikakken yanayin zamantakewar al’ummar Afghanistan.

Har ila yau, wakilin Sin Yue Xiaoyong ya ce, kasar Sin tana goyon bayan bangarorin biyu da ricikin ya shafa, da su gaggauta neman wata dabarar warware matsalar kasar Afghanistan ta hanyar siyasa, da kuma kulla yarjejeniya mai dacewa. (Maryam)