logo

HAUSA

Duniya na bukatar kara azamar ba da rigakafi domin dakile sabon zagayen annobar COVID-19

2021-08-05 17:56:33 cri

Duniya na bukatar kara azamar ba da rigakafi domin dakile sabon zagayen annobar COVID-19_fororder_1

A yayin da duniya ke fuskantar karin bazuwar cutar numfashi ta COVID-19 a sabon zagaye, masharhanta da dama na ganin har yanzu, bukatar nan ta a hada karfi da karfe tsakanin sassan kasa da kasa, domin yakar cutar na nan daram.

Ya zuwa jiya Laraba, a cewar alkaluman cibiyar Johns Hopkins ta Amurka, jimillar adadin wadanda suka harbu da COVID-19 a duniya baki daya ya haura mutum miliyan 200. A kasar Amurka kadai, adadin wadanda suka harbu da cutar ya kai mutum 35,292,721, ciki har da mutum 614,666 da ta hallaka, inda ta zamo kasa dake kan gaba a duniya a wannan fanni da kaso 18 bisa dari na daukacin masu dauke da annobar, da kuma kaso kusan 15 bisa dari na jimillar wadanda cutar ta hallaka a duniya baki daya.

Sauran kasashen dake sahun gaba a alkaluman yaduwar cutar, sun hada da Indiya mai mutum 31,769,132, da Brazil mai 19,985,817. Kaza lika kasashen da ke da masu dauke da cutar sama da miyan 4 a duniya, sun hada da Rasha, da Faransa, da Birtaniya, da Turkiyya, da Argentina. Sauran su ne Colombia, da Sifaniya, Italiya da Iran.

Masharhanta da dama dai na danganta karuwar masu harbuwa da wannan annoba a duniya baki daya, da shiga sabon zangon bazuwar sabbin nau’o’inta, musamman ma nau’in Delta mai saurin bazuwa, da kuma illa ga lafiyar bil adama. Da kuma gibin da ake ci gaba da samu na yiwa karin al’ummun kasashe daban daban rigakafin cutar.

Tuni dai masana, da hukumar lafiya ta duniya WHO, suka sha ba da shawarar gaggauta yiwa karin al’ummun duniya rigakafin wannan annoba, a matsayin hanya daya tilo mafi dacewa, ta dakile yaduwar cutar. Sai dai kawo yanzu, alkaluman da WHO ke fitarwa na nuna “Da sauran rina a kaba”, game da gaggauta yiwa kaso mai yawa na al’ummun duniya rigakafi.

Duk da yake kasar Sin ta yi rawar gani, wajen raba alluran rigakafin wannan cuta ga sassan kasa da kasa, a matsayin gudummawar ta ga yakin da ake yi da annobar, a hannu guda, akwai bukatar sauran kasashe masu wadata dake sarrafa rigakafin a cikin gida, su ma su kara azama wajen samar da tallafin rigakafin ga sauran sassa, ta yadda alluran za su wadata, a kuma kai ga “Gudu tare a tsira tare”, domin kuwa rashin yin hakan, na iya sake baiwa cutar damar kewaya duniya a zagaye na gaba! (Saminu Alhassan)