logo

HAUSA

Gaggawar Sayen Rigakafin Cutar COVID-19 Ta Yi Illa Ga Hadin Gwiwar Duniya Wajen Yaki Da Cutar

2021-01-15 08:56:18 CRI

Gaggawar Sayen Rigakafin Cutar COVID-19 Ta Yi Illa Ga Hadin Gwiwar Duniya Wajen Yaki Da Cutar_fororder_sin

Alkaluman cibiyar dakilewa da kadagarkin cututtuka masu yaduwa ta Afirka sun nuna cewa, ya zuwa ranar Laraba 13 ga wata, mutane 310,7979 sun kamu da cutar COVID-19, yayin da wasu 74,444 suka rasa rayukansu sakamakon cutar. Wasu kasashen Afirka kamar Nijeriya, Afirka ta Kudu, Masar, Zambiya suna kokarinsu kan yiwa al’ummominsu allurar rigakafin cutar ta hanyoyi daban daban.

A matsayinta na kasa da ke sahun gaba a duniya wajen nazarin rigakafin, kasar Sin tana kara azama kan rarraba rigakafin tsakanin kasa da kasa cikin adalci. Tun tuni shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi alkawarin cewa, za a mayar da allurar rigakafin cutar COVID-19 a matsayin kayan al’umma, kuma kasar Sin tana son ganin kasashen Afirka sun ci gajiyar rigakafin kafin sauran kasashe. Kasar Sin ta kuma shiga shirin COVAX. Kwanan baya, na fara samar wa kasashen Brazil, Masar da wasu kasashe rigakafin kirar kasar Sin.

Amma duk da haka, wasu ‘yan siyasan kasashen yammacin duniya sun manta da batun rarraba allurar cikin adalci. Wani rahoton da kawancen sa ido kan allurar rigakafin cututtuka na jama’a ya gabatar ya bayyana cewa, ko da yake jimillar ‘yan kasashe masu kudi ta kai kaso 14 bisa jimilar al’ummomin duniya, amma ya zuwa yanzu, wadannan kasashe sun sayi fiye da rabin allurar rigakafin cutar ta COVID-19 a duniya. Har ma a kasar Canada, yawan allurar rigakafin da kasar ta saya ya fi yawan ‘yan kasar yawa har sau 5. Amma a wani bangare na daban, a kasashen Kenya, Myanmar da sauran kasashe 65 masu karanci da matsakaicin kudin shiga, mutum daya cikin mutane 10 kawai ne ake sa ran za a yiwa allurar kafin karshen wannan shekara.

Kasashen yammacin duniya sun yi ikirarin yaki da annobar cikin hadin gwiwar kasa da kasa, amma ba su nuna sahihanci ko kadan ba. Da ganin saurin karuwar yawan masu kamuwa da cutar a gida, wadannan kasashe sun mayar da rigakafin a matsayin matakin karshe na yaki da cutar, ba su kula da kasashen Afirka, da sauran kasashe marasa ci gaba ba. Sun yi gaggawar sayen rigakafin fiye da yadda suke bukata, lamarin da ya yi babbar illa ga hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da cutar.

Ba za a ga bayan annobar cikin gajeren lokaci ba, har sai kasashen duniya sun hada kansu yadda ya kamata, musamman ma kamata yayi kasashe masu sukuni su yi hangen nesa, su sauke nauyinsu na da’a. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan