logo

HAUSA

CGTN: A Idon Masu Duba Shafin Intanet Kaso 80 Bisa Dari, An Siyasantar Da Batun Gano Asalin Cutar COVID-19

2021-07-27 10:44:39 CRI

CGTN: A Idon Masu Duba Shafin Intanet Kaso 80 Bisa Dari, An Siyasantar Da Batun Gano Asalin Cutar COVID-19_fororder_cuta

A daren ranar 26 ga wata ne dandalin kwararru, na gidan talebijin na duniya na kasar Sin CGTN, ya kaddamar da rahoton binciken ra’ayoyin jama’a a kan yanar gizo, dangane da tambayar “ko an siyasantar da batun gano asalin kwayar cutar numfahi ta COVID-19 ko a’a”.

Rahoton ya shaida cewa, masu duba shafin intanet da yawansu ya kai kaso 80 cikin 100 a duniya, wadanda suka jefa nasu kuri’u suna ganin cewa, an sanya siyasa cikin batun gano asalin kwayar cutar ta COVID-19.

CGTN ta gabatar da tambayar ce a intanet, daga sanyin safiyar ranar 24 ga wata bisa agogon wurin, cikin harsuna 6 da ake amfani da su a MDD, wato Sinanci, da Turanci, da Rashanci, da Faransanci, da harshen Sifaniya da na Larabci.

Yayin da kwararrun CGTN suka tantance amsar masu duba shafin intanet, sun gano cewa, a cikin sharhin masu duba shafin intanet a sassa daban daban na duniya, sun fi ambato wasu kalmomi, wato matsin lamba ta fuskar siyasa, takunkumin Amurka, sa ido da yin mulki kan kafofin yada labaru, biyan diyya, da hana ci gaban kasar Sin.

Ko da yake masu duba shafin intanet da suka amsa tambayoyin da CGTN ya bayar suna zaune a sassa daban daban na duniya, amma sun cimma daidaito cikin gajeren lokaci, yayin da suka ba da nasu sharhi.

Cikin mabambantan harsuna, sun bayyana ra’ayoyinsu iri daya, wato ba a hana yaduwar annobar cutar COVID-19 ta hanyar gano asalin kwayar cutar ba. Da batun gano asalin kwayar cutar, wata dabarar siyasa ce da aka yi domin boye yunkurin Amurka dake kunshe da rashin basira, na hana ci gaban kasar Sin.

Sun nuna cewa, aikin gaggawa da za a yi wajen samun nasarar yaki da annobar shi ne gaggauta yin bincike, da bibiya, tare da yi wa al’umma allurar rigakafi, da ba da isasshen magani. Haka kuma, kasashen duniya na bukatar wani babban tsarin samar da alluran rigakafi.

Har ila yau, masu duba shafin intanet masu amfani da harshen Larabci da dama sun yi kira da a kula da harkokin alluran rigakafi a duniya, sun kuma yi fatan cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar wa al’ummun kasa da kasa alluran rigakafin masu rahusa da inganci. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan