logo

HAUSA

An yi wa al’umma riga-kafin COVID-19 sama da miliyan 763 a duk fadin kasar Sin

2021-06-06 17:28:52 CRI

Hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar a yau Lahadi cewa, an yi wa al’ummar kasar riga-kafin COVID-19 sama da miliyan 763 a duk fadin kasar Sin ya zuwa ranar Asabar.

A ranar Asabar, an samu rahoton shigo da cutar guda bakwai daga ketare, wadanda suka hada da wadanda aka tabbatar sun kamu da kuma wadanda ba sa nuna alamun kamuwa da cutar. A cewar hukumar lafiyar, mutanen sun shigo lardin Guangdong ne daga kasashen Bangladesh, da Cambodia, da Faransa, da Kanada, da Kamaru da kuma Indiya.(Ahmad)

Ahmad