logo

HAUSA

Kasar Sin ta nuna rashin amincewa da kudirin doka mai nasaba da Taiwan da Amurka ta amince da shi

2021-08-12 19:35:21 CRI

Kasar Sin ta bayyana rashin jin dadinta da babbar murya, tare da yin watsi da amincewar da majalisar dattawan Amurka ta yi, kan wani kudirin doka da zai baiwa yankin Taiwan damar shiga harkokin hukumar lafiya ta duniya(WHO).

A ranar 6 ga watan Agusta ne, majalisar dattawan Amurkar ta amince da kudirin dokar, inda a cikinsa ta umarci sakataren harkokin wajen Amurka, da ya fito da wani tsari da zai dawowa da yankin na Taiwan matsayinsa na zama ‘yar kallo a WHO, inda ya samu amincewar ‘yan majalisar kalilan dake zama a lokacin. Kudirin ya bukaci sakataren harkokin wajen na Amurka, da ya bayyana sauye-sauye da yadda za a inganta shirin ma’aikatar harkokin wajen, ta yadda za a goyi bayan matsayin yankin a matsayin ‘yar kallo a babban taron kiwon lafiya na duniya(WHA).

Sai dai mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta kira kudirin dokar, a matsayin wani mataki na siyasa da wasu ‘yan siyasa makiya kasar Sin suka kitsa, kuma hakan ya saba manufar kasar Sin daya tak a duniya, da sanarwoyin hadin gwiwa guda uku da Sin da Amurka suka cimma, baya ga saba dokokin kasa da kasa, da muhimman ka’idoji da suka shafi alakar kasashen duniya, kana tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar Sin.

A don haka, Madam Hua, ta bukaci majalisar dattawan Amurka, da ta daina taimakawa yankin Taiwan da sunan fadada tasirinsa, ta kuma daina aikewa da mummunan sako ga masu neman ‘yancin yankin na Taiwan.(Ibrahim)

Ibrahim