logo

HAUSA

Sin ta yi Allah wadai da shirin Amurka na sayarwa Taiwan makamai

2021-08-05 20:53:27 CRI

Sin ta yi Allah wadai da shirin Amurka na sayarwa Taiwan makamai_fororder_95eef01f3a292df550c32f8cf4dfb56835a8731a

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya ce kasar sa ta yi Allah wadai da matakin Amurka, na amincewa ta sayarwa yankin Taiwan na kasar Sin makaman yaki, kuma Sin ta gabatar da wakilci ga tsagin Amurka domin bin bahasin al’amarin. Kakakin ya ce Sin za ta dauki matakan da suka wajaba, na martani gwargwadon halin da ake ciki.

Ofishin lura da harkokin hadin gwiwar tsaro na hukumar tsaron Amurka Pentagon, shi ne ya sanar a jiya Laraba cewa, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta amince a sayarwa Taiwan, matsakaitan motocin yaki samfurin Atilari guda 40, kan kudi da suka kai dala miliyan 750.

A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Taiwan yanki ne na kasar Sin da ba za a iya balle shi ba, kuma matakin Amurka na yunkurin sayarwa yankin makamai, tsoma hannu ne cikin harkokin gidan kasar Sin, kuma hakan ya ci karo da moriyar kasar Sin ta fuskar wanzar da tsaro, da kare ikon mulkin yankunan ta.  (Saminu)