Kasar Sin ta yanke shawarar dawo da jakadanta dake Lithuania
2021-08-10 20:31:54 CRI
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana cewa, kasarsa ta yanke shawarar dawo da jakadanta dake Lithuania zuwa gida, tare da bukatar gwamnatin Lithuania da ita ma da janye nata jakadan dake kasar Sin.
A baya-bayan nan dai, gwamnatin Lithuania ta sanar da shawarar barin mahukuntan yankin Taiwan na kasar Sin, su bude ofishin wakilci da sunan Taiwan a kasarta, duk da rashin amincewa da kasar Sin din ta sha nunawa da ma matakin da hakan zai haifar.
Kakakin ya ce, bangaren kasar Sin, ya gargadi bangaren Lithuania cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma jamhuriyar jama’ar kasar Sin, ita ce halattiyar gwamnati dake wakiltar kasar Sin baki daya. Kuma manufar kasar Sin daya tak, ta samu amincewar ka’idoji na alakar kasa da kasa da ma duniya baki daya. Kana shi ne ginshikin siyasa na kasar Sin game da raya hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashe.
A don haka, kasar Sin tana kira ga bangaren Lithuania, da ya hanzarta gyara kuskuren da ya yi, ya kuma dauki matakan da suka dace, don gyara wannan barna, don kar ya kara fadawa hanyar da ba ta dace ba.(Ibrahim)
Labarai Masu Nasaba
- Sin ta nuna rashin amincewa da yadda firaministan Japan ya kira Taiwan da kasa mai cin gashin kai
- Majalisar kiwon lafiyar duniya ta yi watsi da batun dake shafar Taiwan
- Kasar Sin ta nanata adawarta da halartar yankin Taiwan babban taron hukumar lafiya ta duniya
- Yaushe Ne ‘Yan Siyasan Amurka Za Su Daina Goyon Bayan Taiwan Ta Halarci Babban Taron WHO?