logo

HAUSA

Kasar Sin za ta mayar da martani mai karfi idan Amurka ta sayarwa yankin Taiwan makamai

2021-08-05 22:17:28 CRI

Kasar Sin za ta mayar da martani mai karfi idan Amurka ta sayarwa yankin Taiwan makamai_fororder_A

Ma’aikatar tsaron Amurka ta sanar a jiya Laraba cewa, kwanan nan ne ma’aikatar harkokin wajen kasar ta amince da wani shiri na dala miliyan 750, game da sayarwa yankin Taiwan na kasar Sin makamai, al’amarin da ya zama karon farko da wannan gwamnati dake karkashin jagorancin Joe Biden ta sanar da shirin ta na sayar da makamai ga Taiwan.

Wannan danyen aikin, ba kawai zai lalata ikon mallakar yanki da moriyar tsaron kasar Sin gami da saba wa dokokin kasa da kasa ya yi ba, har ma ya sabawa babbar manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duiya, gami da wasu sanarwa uku da aka daddale tsakanin Sin da Amurka cikin hadin-gwiwa.

Kasar Sin tana matukar adawa da wannan shirin na Amurka, kuma ko shakka babu, za ta dauki wani matakin da ya wajaba wajen mayar da martani.

Tun bayan da sabuwar gwamnatin Amurka ta kama aiki ya zuwa yanzu, ko kadan ma ba ta gyara kura-kuran da tsohuwar gwamnatin kasar ta yi a kan batun Taiwan ba, har ma tana ci gaba da aikata kura-kurai. Wannan shiri na sayarwa yankin Taiwan makamai da Amurka ta amince da shi kwanan nan, zai haifar da bababr matsala ga halin da ake ciki a yankin Taiwan. Kuma kowa zai fahimci cewa, Amurka ce ke haifar da babbar illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan, kuma ita ce ke kirkiro babban hadarin tsaro a wurin.

Babu wani mutum ko wata kasa da za su iya kawo tarnaki ga dunkule kasar Sin baki daya. Kuma ya zama dole Amurka ta mutunta babbar manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da soke shirin ta na sayarwa Taiwan makamai, da katse duk wata huldar soja tsakaninta da yankin. (Murtala Zhang)