logo

HAUSA

Wajibi Ne Lithuania Ta Hanzarta Gyara Kuskurenta Ba Tare Da Bata Lokaci Ba

2021-08-11 20:06:18 CRI

Kwanan baya, kasar Lithuania ta saba wa tanade-tanaden da ke cikin sanarwar kulla huldar diplomasiyya a tsakaninta da kasar Sin, inda ta amincewa mahukuntan yankin Taiwan kafa ofishinsa a Vilnius, babban birnin Lithuania da sunan “Taiwan”. Don haka a ranar 10 ga wata, kasar Sin ta sanar da dawo da jakadanta daga Lithuania, tare da bukatar gwamnatin Lithuania da ita ma ta dawo da jakadanta zuwa gida. Matakin diflomasiya da kasar Sin ta dauka, wanda ba ta taba yin haka ba, ya nuna cewa, duk wanda ya gurgunta ikon mulki da cikakkun yankunan kasar Sin, tabbas kasar Sin za ta mayar masa da martani mai karfi.

Sanin kowa ne cewa, Lithuania wadda ke dogaro da Amurka ta fuskar tsaron kasa, tana yunkurin faranta ran Amurka ne kawai, da zummar daga matsayinta cikin manyan tsare-tsaren Amurka kan kasar Sin, ta haka Amurka za ta biya bukatun Lithuania. Amma Lithuania ta kambama kanta, matakin da ta dauka, ya tona rashin hangen nesa da ‘yan siyasan Lithuania suka nuna.

Yanzu abu mafi muhimmanci ga Lithuania shi ne kara fahimtar muhimmancin manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, wadda shi ne tushe na siyasa wajen raya hulda a tsakanin kasar Sin da kasashen duniya. Haka kuma gwamnatin Sin da jama’ar Sin ba su sauya aniyar dinke kasar Sin baki daya ba. Ba su yarda a gurgunta ikon mulki da cikakkun yankunan kasa ba. Ya zama tilas Lithuania ta hanzarta gyara kuskurenta ba tare da bata lokaci ba, ta dauki hakikanin matakai, ta rage illoli masu ruwa da tsaki, kada ta kara fadawa hanyar da ba ta dace ba. Haka kuma ba wanda zai iya hana dinkuwar kasar Sin baki daya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan