logo

HAUSA

Amurka Ta Cancanci Zama Kasa Ta Farko A Duniya Wadda Ta Gaza Yaki Da Annobar COVID-19

2021-08-12 21:11:46 CRI

Yanzu Amurka tana samun karuwar masu kamuwa da annobar cutar numfashi ta COVID-19 bayan da cutar ta sake barkewa a zagaye na 4. Alkaluman kididdiga da jaridar The New York Times ta fitar a kwanan baya sun nuna cewa, a makon da ya gabata, matsakaicin yawan sabbin masu kamuwa da cutar a Amurka a kowace rana, ya zarce dubu 118, kuma matsakacin yawan sabbin wadanda ke kwanciya a asibiti a kowace rana ya wuce dubu 66. Asibitoci da dama a Amurka cike suke da majinyata. Ya zuwa ranar 11 ga wata, yawan masu kamuwa da cutar a Amurka, ya wuce miliyan 36 baki daya, yayin da mutane fiye da dubu 610 suka rasa rayukansu. Dukkan wadannan alkaluma sun zama na farko a duniya.

An yi wa Amurka ba’a sosai da ganin irin wannan hali na ban tausayi da take ciki, wadda kamfanin dillancin labaru na Bloomberg News ya ayyana ta a matsayin kasa ta farko a duniya wajen yaki da annobar. Kana kuma irin wannan hali na ban tausayi da ake ciki a Amurka, ya sanya Amurka ta cancanci zama kasa ta farko a duniya wadda ta gaza yaki da annobar, kamar yadda rahoto mai lakabin “Amurka na sahun gaba?! Gaskiyar halin da kasar ke ciki ta fannin tinkarar annobar COVID-19”, wanda dandalin kwararru guda 3 na kasar Sin suka fitar a kwanan baya ya bayyana.

Idan mun waiwayi abubuwan da suka faru a Amurka, a fannin yaki da annobar a shekara guda da ta gabata, to, za a iya fahimtar cewa, yadda masu mulkin kasar suka mayar da kare moriyar siyasa a gaban rayukan al’umma, ya sanya Amurka ta gaza yaki da annobar.

Samun moriyar siyasa yana gaban kome, yayin da rayukan al’umma suka zama maras ma’ana. Irin wannan tunani na rashin tausayi, ya haifar da jerin matakai masu ban mamaki a Amurka. Tsohon shugaban Amurka ya fi yada bayanan karya kan annobar. An matsa wa masana kimiyya da kwararru wadanda suka fadi gaskiya lamba. An rika baza karya kan asalin kwayar cutar COVID-19 tare da dora wa wasu laifi, har ma an dora wa wasu kasashe laifin barkewar annobar. Amma Amurka ta kau da kai kan dakile yaduwar annobar, har ma ta bar annobar tana yaduwa a duniya.

Amurka ba ta dakile yaduwar annobar a cikin gidanta ba, kuma ta bartana hadin gwiwar kasa da kasa. Abubuwan da Amurka ta yi sun shaida cewa, barkewar annobar, wani bala’i ne, amma ta zama hadari a Amurka. Kamar yadda William Foege, mai ilmin cututtuka masu yaduwa na Amurka kuma tsohon darektan cibiyar dakile da kandagarkin cututtukan Amurka ya fada, annobar COVID-19, ta yi kama da wani nau’in kisan kiyashi. Haka kuma, a watan Yunin bara, mujallar The Atlantic ta Amurka ta ce, muna rayuwa ne cikin wata kasa wadda ta gaza yin kome. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan