logo

HAUSA

Kalubalantar Kimiyya Ta Sa Amurka Tana Girban Mummunan Sakamakon Aiki Da Ta Yi

2021-08-11 20:38:28 CRI

A bara madam Patrice A. Harris, tsohuwar darektar hadaddiyar kungiyar ilmin likitancin kasar Amurka ta taba yin gargadin cewa, yayin da muke yaki da annobar COVID-19, dole ne mu mayar da kwayar cutar a matsayin abokin gaba, a maimakon mayar da kimiyya kamar abokin gabanmu. Amma abin bakin ciki shi ne, ya zuwa yanzu irin wannan ra’ayi na sanin ya kamata bai samu amincewa sosai a Amurka ba tukuna. Sakamakon kare moriyar siyasa, da takarar da ke tsakanin jam’iyyu, ya sa wasu ‘yan siyasan Amurka suke kalubalantar Ilimin kimiyya, lamarin da ya ba wa duniya mamaki sosai, a don haka, tabbas Amurka za ta girbi mummunan sakamakon aiki da ta yi.

A cikin rahoto mai lakabin “Amurka na sahun gaba?! Gaskiyar halin da kasar ke ciki ta fannin tinkarar annobar COVID-19”, wanda dandalin kwararru guda 3 na kasar Sin suka fitar a kwanan baya, an yi karin bayani kan kuskuren da Amurka ta yi a fannonin dakile da kandagarkin annobar, matakan da ta dauka da aikin gano asalin annobar. Rahoton ya sanya kasashen duniya su kara sanin cewa, kalubalantar kimiyya da fasaha, shi ne dalilin da ya sa Amurka, a matsayinta na kasa mafi karfi a duniya, ta zama kasa ta farko a duniya wadda ta gaza yaki da annobar.

Annobar ta COVID-19 ta barke ne a shekarar da aka yi babban zaben shugaban kasa a Amurka, jam’iyyu 2 na Amurka sun yi amfani da barkewar annobar, wajen bata sunan juna da neman samun karin kuri’u. Galibi dai hakan ya kara tsanantar rashin sanin ya kamata a Amurka. An siyasantar da batutuwa da dama a Amurka, wadanda a baya suke da nasaba da kimiyya kawai, alal misali, ko a sanya marufin baki da hanci ko a’a, ko a yi riga kafi ko a’a, ko a goyi bayan ba da tazara yayin mu'amala da juna ko a’a.

Har ila yau kuma, wasu ‘yan siyasan Amurka sun kalubalanci kimiyya a fannin gano asalin annobar. Yayin da annobar take bazuwa a cikin gida, gwamnatin Amurka ba ta yi tunanin matakan da za ta dauka ba, ta ci gaba da kara gishiri kan bullar annobar COVID-19 daga dakin gwaji, ta rika dora wa wasu laifi, a yunkurin mayar da baki fari.

Don ganin ta cimma wannan manufa, gwamnatin Amurka ta umurci hukumomin leken asiri, su shiga aikin gano asalin annobar, tare da fitar da sakamako cikin kwanaki 90. Sa’an nan kuma ta matsa wa hukumar lafiyar duniya wato WHO lamba, don ta kaddamar da aikin gano asalin annobar a zagaye na biyu a kasar Sin, ta kuma yi yunkurin dora laifin barkewar annobar kan kasar Sin. Wasan mataki na siyasa da Amurka take amfani da shi ya nuna cewa, wasu Amurkawa ba sa jin kunya ko kadan, suna kalubalantar kimiyya, sun kau da kai daga ceton rayukan mutane. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan