logo

HAUSA

Masanan Amurka sun yi kira ga gwamnatin kasarsu da ta fitar da alluran rigakafin COVID-19 zuwa ketare

2021-08-12 11:02:27 CRI

Masanan Amurka sun yi kira ga gwamnatin kasarsu da ta fitar da alluran rigakafin COVID-19 zuwa ketare_fororder_hoto2

A ranar 10 ga wata, masana harkokin kiwon lafiya, da kwarrau a fannin kimiyya da fasaha, da kuma wasu shugabannin kungiyoyi na kasar Amurka sama da guda 175, da hukumomi sama da guda 50, sun aike da wasikar hadin gwiwa ga shugaban kasar Amurka Joseph Biden, inda suka yi kira ga gwamnatin Amurka, da ta dauki matakan habaka aikin hada-hadar alluran rigakafin COVID-19, da kuma fitar da alluran rigakafi zuwa ketare, domin biyan bukatun al’ummomin kasa da kasa, ta yadda za a kawar da matsalar fitowar sabbin nauyoyin kwayoyin cutar COVID-19.

Cikin wasikar, sun ce, suna fatan cikin watanni shida masu zuwa, gwamnatin kasar Amurka za ta kafa masana’antun da za su iya samar da alluran rigakafin COVID-19 samfurin mRNA biliyan 8 a kowace shekara, da kuma sanar da shiri mai nasaba da hakan cikin wata daya. A sa’i daya kuma, sun yi kira ga gwamnatin kasar, da ta kafa azuzuwan horaswa kan fasahohin sarrafa alluran rigakafin COVID-19, da kuma mika fasahohin ga masu bukata.

Haka kuma, sun bukaci gwamnatin kasar da ta fitar da alluran rigakafi zuwa kasashen ketare, bisa shirin COVAX, ko sauran shirye-shirye masu nasaba da hakan, don ta fitar da alluran rigakafi a kalla miliyan 10 zuwa kasashen ketare cikin mako daya. (Maryam)