Hua ta bukaci kasashen da abin ya shafa su martaba ikon mulkin kasar Sin ta fuskar aiwatar da doka
2021-08-12 21:02:00 CRI
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hua Chunying, ta bukaci kasashen da abin ya shafa, da su martaba doka, da ‘yancin shari’a na kasar Sin, su kuma daina furta kalaman da ba su dace ba.
Kalaman Madam Hua na zuwa ne, bayan da kasar Canada ta zargi hukuncin da kasar Sin ta yanke game da shari’ar da ta shafi ‘yan kasar Canadan guda biyu. Michael Spavor wanda aka yanke wa hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekaru 11 saboda aikata laifin leken asiri, da kuma Robert Lloyd Schellenberg wanda aka yanke wa hukuncin kisa, saboda fasa kwaurin miyagun kwayoyi. Kungiyar tarayyar Turai da kasar Birtaniya sun nuna goyon bayansu ga kasar Canada. Yanzu haka dai, kasar ta Canada, tana hada kai da wasu tsirarun kasashe, a yunkurin ganin sun mayar da fari baki, inda suke kokarin yin fatali da shaidu. Har suna nuna yatsa ga kotunan da abin ya shafa dake kasar Sin, bisa hukuncin da suka yanke wa ‘yan kasar ta Canada, wanda hakan tamkar tsoma baki ne a harkokin shari’ar kasar Sin, lamarin da ya saba tsarin doka. Kuma kasar Sin ta yi Allah wadai da shi.
Madam ta ce, an kama Schellenberg ne da laifin safarar miyagun kwayoyi tsakanin kasa da kasa, da sumogan sama da kilogram 222 na methamphetamine. Adadin kwayar a shari’ar da ake yi, musamman tana da yawa. Shi kuwa Michael Spavor, an yanke masa hukunci ne, bisa laifin keta harkokin tsaron kasar Sin, An saurari kararsa a watan Maris din shekarar da ta gabata, kamar yadda doka ta tanada. Madam Hua tana mai cewa, babu wani dan kasar waje, da zai iya zama kamar wanda ya fi karfin doka. Ta ci gaba da cewa, kasar Sin, kasa ce mai bin doka, kana hukumominta na shari’a suna hukunta duk wani bata gari ba tare da nuna wani bambanci ba, suna kuma yanke hukunci kan dukkan laifuffunkan da aka aikata bisa doka, ba tare da nuna bambanci kan kasar da mutum ya fito ba.(Ibrahim)
Labarai Masu Nasaba
- Wakilin Sin: Ya kamata majalisar kare hakkin dan-Adam ta MDD ta mayar da hankali kan yadda ake take hakkin mata da ‘yan mata ‘yan asalin kasar Canada a kasar
- An sake gano karin gawawwaki 182 a kusa da wata tsohuwar makaranta dake mazaunin ’yan asalin kasar Canada
- Wasu tambayoyi uku ga firaministan kasar Canada
- Dole ne a yi cikakken bincike game da manyan laifuka a kan ‘yan asalin kasar Canada