logo

HAUSA

Wasu tambayoyi uku ga firaministan kasar Canada

2021-06-27 22:09:23 CRI

Wasu tambayoyi uku ga firaministan kasar Canada_fororder_微信图片_20210627183030

Kwanan baya, an gano wasu kaburbura 751 a wata makarantar kwana da ke lardin Saskatchewan na kasar Canada, kari kan wasu gawarwakin yara ‘yan asalin kasar 215 da aka gano a wata makarantar kwana da ke lardin British Columbia na kasar a ranar 28 ga watan da ya gabata.

Lalle yadda aka gano gawarwaki kusan dubu cikin lokacin da bai kai wata guda ba, ya firgita al’ummar duniya, baya ga kuma ya sa wata babbar ayar tambaya, shin kaburbura irin wannan nawa ne suka rage a kasar? Kuma yara ‘yan asalin kasar nawa ne aka ci zarafinsu har suka mutu?

Bayan da aka ba da labarin lamarin, nan da nan sai firaministan kasar Canada Justin Trudeau ya fitar da sanarwa, inda ya bayyana bakin cikinsa game da wannan mummunan abin da ya faru ga ‘yan asalin kasar. Duk da haka, akwai bambanci tsakanin furucin da ya yi da ma matakan da ya dauka. A farkon kama mukaminsa, firaministan ya lashi takobin mai da sassautawa tare da ‘yan asalin kasar a matsayin babban aiki na farko a gare shi, amma ga shi cikin shekaru kusan shida da suka wuce, an dauki matakan da ba su kai kaso 1/10 ba bisa alkawuran da ya dauka.

A sakamakon matsin lambar da ya fuskanta, Mr.Trudeau ya juya ga Paparoma, inda ya bukace shi da ya je kasar Canada tare da neman gafara dangane da lamarin. Amma yadda Mr.Trudeau ke neman karkata hankalin al’umma ya sa mana tambaya dangane da niyyar gwamnatin kasar wajen daidaita matsalarta da ma ko da gaske ne za a kai ga kyautata yanayin da ‘yan asalin kasar ke ciki.

Abin da ya fi ba mu damuwa shi ne, gwamnatin Canada ta yi biris da matsalar hakkin dan Adam da take fuskanta, har ma ta zama barawon da ke kiran kama barawo. A kwanan baya, a gun taro karo na 47 na kwamitin kula da hakkin bil Adam na MDD, a madadin kasashe da dama ne, kasar Sin ta bayar da sanarwar hadin gwiwa, inda ta yi kira da a gudanar da bincike a laifukan da kasar Canada ta aikata wa‘yan asalin kasar. Sanarwar da daga bisani Mr. Trudeau ya mayar da martani a gun wata taron manema labarai da aka gudanar a birnin Ottawa, inda a maimakon ya mai da hankali a kan batun ‘yan asalin kasarsa, sai ya zargi kasar Sin da keta hakkin bil Adam a jihar Xinjiang. Amma tambaya ita ce, shin ina ne shaidu game da batu na wai keta hakkin bil Adam a Xinjiang?

Sanin kowa ne al’ummar American Indian da Inuit su ne ‘yan asalin kasar Canada, wadanda baki Turawa suka kashe su da ma kore su daga kasarsu, tare da kwace kasa da ma arziki da suka mallaka, daga baya an kafa kasar Canada karkashin jagorancin Turawa fararen fata. Sai kuma aka kafa makarantun kwana ga yara ‘yan asalin kasar, don su yi watsi da ainihin al’adunsu. Daga shekarun 1840 zuwa 1990, yara ‘yan asalin kasar a kalla dubu 150 ne aka raba su da iyayensu tare da tura su makarantun, inda aka ci zarafinsu, har ma yara sama da 4000 sun mutu.

Duk da cewa, an rufe irin wadannan makarantu, amma irin yanayin da ‘yan asalin kasar ke ciki bai sauya ba, duba da cewa, har yanzu fararen fata ke mallakar akasarin filaye da ma albarkatun wannan kasa, a yayin da ake ci gaba da nuna wariya ga‘yan asalin kasar. Alakaluman da aka samar sun nuna cewa, laifukan da aka aikatawa ‘yan asalin kasar ya zarce na wadanda ba‘yan asalin kasar ba da kimanin kaso 58%.

Tarihi ya kasance tamkar madubi ne. Abin bakin ciki shi ne, har yanzu gwamnatin kasar ba ta dauki matakan da suka kamata dangane da yanayin da ‘yan asalin kasar ke ciki. Bayyana bakin ciki ba zai taimaka ga daidaita matsalar ba, in dai gwamnatin kasar tana da niyya, lalle ya kamata Mr.Trudeau ya amsa wasu tambayoyi uku, yaushe ne za a fara bincike kan lamarin? Yaushe ne za a biya diyya ga ‘yan asalin kasar? Sai kuma yaushe ne za a kaddamar da hakikanin matakai na daidaita wariyar kabilun kasar?