logo

HAUSA

Wakilin Sin: Ya kamata majalisar kare hakkin dan-Adam ta MDD ta mayar da hankali kan yadda ake take hakkin mata da ‘yan mata ‘yan asalin kasar Canada a kasar

2021-07-07 11:09:42 CRI

Wakilin Sin: Ya kamata majalisar kare hakkin dan-Adam ta MDD ta mayar da hankali kan yadda ake take hakkin mata da ‘yan mata ‘yan asalin kasar Canada a kasar_fororder_20210706212421488

Minista a tawagar kasar Sin dake ofishin MDD a Genava Jiang Duan, ya nuna damuwa matuka, game da yadda aka keta hakkin mata da ‘yan mata ‘yan asalin kasar Canada a kasar.  Jami’in ya yi wannan kira ne, yayin jawabin da ya gabatar, a wani taron karawa juna sani na shekara-shekara game da ‘yancin mata da aka shirya, yayin taron majalisar kare hakkin dan-Adam ta MDD karo na 47. Jiang Duan ya kuma yi nuni da cewa, a kwanakin baya, bi da bi ne aka gano kaburbura da gawawwaki sama da dubu, a cikin harabar wasu makarantun kwana na ‘yan asalin kasar. Bayanai na nuna cewa, an ci zarafin yara ‘yan asalin kasar Canada da dama ta hanyar lalata a makarantun kwana.

Haka kuma, kasar Canada ta dauki matakan tilas don hana mata da ‘yan mata ‘yan asalin kasar wajen daukar ciki. A don haka kasar Sin, tana kira da a gudanar da cikakken bincike ba tare da nuna wani son kai ba, kan dukkan zargin da ake yiwa kasar ta Canada da aikatawa, kan mata da ‘yan mata ‘yan asalin kasar, don tabbatar da cewa, an hukunta dukkan wadanda ke da hannu a aikata wannan danyen aiki.

Jiang ya ce, kasar Canada, ba hakuri kadai za ta bayar kan wannan aika-aika ba, wajibi ne ta dauki mataki a zahiri, ta kuma gyara kuskuren da ta aikata. Haka kuma kasar Sin ta bukaci Canada, da ta magance matsalar karuwar nuna wariyar launin fata, da laifuffukan nuna kyama kan ‘yan Afirka da ‘yan asalin Afirka, da na Asiya, musamman mata da ‘yan mata.(Ibrahim)