logo

HAUSA

Dole ne a yi cikakken bincike game da manyan laifuka a kan ‘yan asalin kasar Canada

2021-06-23 21:21:38 cri

Jiya Talata, a yayin zama na 47 na Kwamitin Kare Hakkin Dan-Adam na Majalisar Dinkin Duniya, kasar Sin ta wakilci kasashen Rasha, Belarus, Koriya ta Arewa, Iran, Syria da sauransu, don yin jawabi na hadin gwiwa kan batun hakkin dan adam na kasar Canada, inda suka bukaci Canada da ta hanzarta dakatar da take hakkin dan adam.

Jawabin na hadin gwiwar ya nuna cewa, kasar Canada ta aikata laifuka daban-daban kan ‘yan asalin kasar a tarihi, ciki har da kwace kasa, kashe rayuka, kawar da al'adu da sauransu.

Kwanan nan, an sami ragowar gawar yara Indiyawan 215 ‘yan asalin kasar Canada a wurin da wata tsohuwar makarantar kwana take a kasar, kuma ba a rubuta mutuwar wadannan yara ba.

Lorelei Williams, 'yar gwagwarmayar kare hakkin ‘yan asalin kasar Canada, ta nuna cewa, wannan lamarin "kusurwa kawai ta dutsen kankara." A zahiri, an gudanar da tsarin makarantar kwana na ‘yan asalin kasa a Canada fiye da karni guda. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka bayar an ce, an tilasta sama da kananan yara ‘yan asalin kasar su 150,000 barin iyayensu, kuma suka shiga cikin "makarantun kwana na Indiya", wadanda sama da dubu 50 aka azabtar har suka mutu.

Ko da yake wasu 'yan siyasan kasar Canada sun ce wai zaluncin da aka yi wa 'yan asalin kasar sun zama tarihi. Amma, hakikanin halin da ake ciki shi ne, ba su taba mayar da hankali ba game da batutuwan da suka shafi hakkin dan adam, ciki har da take hakkin 'yan asalin kasar, da nuna wariyar launin fata, har ma sun shagwaba kan haka.

Ga misali, lokacin da Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya ya zartar da sanarwar Majalisar Dinkin Duniya kan 'Yancin' Yan Asalin a shekarar 2007, yawancin kasashe mambobin sun jefa kuri’ar amincewa, amma kasar Canada, tare da wasu kasashe kalilan kamar Amurka, sun jefa kuri’ar adawa, har sai a shekarar 2016 ta janye adawarta.

Rayuwar 'yan asalin kasa kuma rayuwa ce. Daga tarihi zuwa hakikanin hali, kasar Canada tana cin zarafi da aikata laifuka da yawa a fagen hakkin dan adam. Don haka ba ta cancanci yin zargi ga sauran kasashe a fannin kare hakkin dan adam ba. (Mai fassara: Bilkisu)