logo

HAUSA

An sake gano karin gawawwaki 182 a kusa da wata tsohuwar makaranta dake mazaunin ’yan asalin kasar Canada

2021-07-01 09:50:26 CRI

An sake gano karin gawawwaki 182 a kusa da wata tsohuwar makaranta dake mazaunin ’yan asalin kasar Canada_fororder_210701-saminu 1-Canada school

A jiya Laraba ne aka gano karin gawawwaki 182 da aka binne, a wata tsohuwar makarantar kwana ta ’yan asalin kasar Canada. Rahotanni sun ce an gano gawawwaki ne, a kusa da yankin Cranbrook dake lardin British Columbia.

Makarantar dai ta kasance karkashin kulawar majami’ar Katolika, tsakanin shekarar 1912 zuwa farkon shekarun 1970. Kuma tuni aka mayar da ginin ta zuwa wurin shakatawa da kulaf din caca, tare da filin wasan kwallon gora a gefensa.

Kafin gano gawawwakin na wannan karo, an gano wasu gawawwakin da aka yi kiyasin sun kai 215, a daura da wata makarantar kwana ta ’yan asalin kasar, da kuma wasu boyayyun kaburbura 751, a kusa da wata makarantar al’ummar Indiyan daji dake Saskatchewan.

Tarihi ya nuna cewa, adadin yaran al’ummu ’yan asalin Canada 150,000 ne suka halarci irin wadannan makarantun kwana a wadancan shekaru. An kuma yi zargin cewa, makarantun na karbar dalibai fiye da kima, inda dalibai ke rayuwa cikin yanayi maras kyau ta fannin muhalli da abinci, suna kuma fama da ayyuka na kaskanci.

A hannu guda kuma, ana yiwa daliban mummunan horo, idan aka same su da laifin yin magana da yaren su na asali, ko idan suka halarci wani biki da ke da nasaba da al’adun su na asali.  (Saminu)