logo

HAUSA

Masanin kasar Amurka: Kasar Amurta ta siyasantar da batun binciken asalin cutar COVID-19 don neman hana ci gaban kasar Sin

2021-08-11 16:16:45 CMG

Masanin kasar Amurka: Kasar Amurta ta siyasantar da batun binciken asalin cutar COVID-19 don neman hana ci gaban kasar Sin_fororder_20210811-Amurka-asalin cuta-Bello

Ko da yake kasar Amurka na fama da saurin karuwar masu kamuwa da cutar COVID-19 a cikin gida, amma tana ci gaba da tsayawa kan yunkurin binciken asalin cutar COVID-19 a sauran kasashe, inda wasu ’yan siyasan kasar ke ayyana batun a matsayin wata maganar siyasa. Dangane da batun, wani masanin ilimin al’amuran duniya na kasar Amurka ya ce, hakan ya nuna cewa, kasar Amurka ta mai da aikin binciken gano asalin cutar a matsayin wani mataki na siyasa, inda ta yada jita-jitar cewa “asalin cutar COVID-19 na daga cikin dakin gwajin halittu na birnin Wuhan na kasar Sin” don dora wa kasar Sin laifi, gami da yunkurin hana ci gaban kasar.

Yayin da yake hira da wakilin kamfanin CMG, John F. Copper, farfesa mai nazarin al’amuran duniya na jami’ar Rhodes College, ya ce, ana samun tsamin dangantaka tsakanin kasashen Amurka da Sin a wadannan kwanaki, don haka kasar Amurka tana damuwa sosai kan cewar, saurin tasowar kasar Sin zai ba ta damar zarce kasar Amurka a fannin samar da tasiri a duniya. Saboda haka kasar Amurka na ta kokarin daukar matakai daban daban don hana ci gaban kasar Sin. Kana daya daga cikin matakan, shi ne dora wa kasar laifi, wanda ya kasance abun da gwamnatin shugaba Biden na kasar Amurka ke kokarin aikatawa. (Bello Wang)

Bello