logo

HAUSA

Amurka: Takara A Tsakanin Jam'iyyu Ta Haifar Da Bala’in Jin Kai A Kasar

2021-08-10 21:19:47 CRI

Kwanan baya, kamfanin dillancin labaru na Bloomberg News na kasar Amurka ya ayyana kasar Amurka a matsayin kasa ta farko a duniya wajen yaki da annobar COVID-19. Dangane da lamarin, a ranar 9 ga wata, dandalin kwararru guda 3 na kasar Sin sun fitar da wani rahoto mai lakabin “Amurka na sahun gaba?! Gaskiyar halin da kasar ke ciki ta fannin tinkarar annobar Covid-19”, inda suka bayyana hakikanin halin da ake ciki a Amurka wajen yaki da annobar, bisa nazarin da suka yi a tsanake da kuma cikakkun bayanai bisa sanin ya kamata. Rahoton ya musunta karyar wai “Amurka ce ta farko a duniya wajen yaki da annobar”, ya kuma sanya kasashen duniya kara sanin yadda jam’iyyun Amurka suka sadaukatar da rayukan al’ummar Amurka wadanda ba su ji ba ba su gani ba.

Ya zuwa yanzu, yawan mutanen da suka kamu da annobar ta COVID-19 a Amurka ya zarce miliyan 35, yayin da wasu fiye da dubu 610 suka rasa rayukansu, dukkan alkaluma sun kasance a kan gaba a duniya. Barkewar annobar ta kasance wani bala’i ga Amurkawa, kana mummunan hadari da ya auku a kasar. Takarar da ke tsakanin jam’iyyun Amurka ta siyasantar da annobar, ya sanya al’ummar Amurka rasa rayukansu, wadanda bai kamata su mutu ba.

A farkon lokacin barkewar annobar, gwamnatin Amurka ta sha kau da kai daga gargadin barkewar annobar, tare da neman rage barazanar da annobar ke kawowa, a kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arziki da samar da guraben aikin yi, ta yadda za ta sake lashe babban zaben shugabancin kasar. Yayin da annobar take bazuwa a jihar New York da California, inda jam’iyyar Democratic ke mulki, ‘yan jam’iyyar Democratic sun mai da hankali sosai wajen sukar ‘yan jam’iyyar Republican, a maimakon yaki da annobar. Yin takara ta fuskar siyasa ya sanya sarkakiyya a manufofin Amurka na yaki da annobar da kuma kawo cikas kan matakan Amurka, ta haka watanni 6 ke nan bayan barkewar annobar a Amurka, gwamnatin Amurka ba ta tsara manyan tsare-tsaren bai daya ba. Amurka ta sha bata lokaci. Amurkawa sun rasa rayukansu sakamakon takarar siyasa tsakanin ‘yan siyasan kasar.

Yanzu haka bala’in jin kai na ci gaba da yaduwa a Amurka. Ya zuwa ranar 9 ga wata, matsakaicin yawan mutane masu kamuwa da annobar COVID-19 a Amurka a kowace rana ya wuce dubu 100 a kwanaki 3 a jere, wanda ya karu da kaso 35 cikin dari bisa na makon jiya. Amurka tana ci gaba da kau da kai daga hakkokin jama’arta, tana ci gaba da yin takarar siyasa. Kome mene ne, ba ta cancanci “kasa ta farko a duniya wajen yaki da annobar” ba. Sai dai“kasa ta farko a duniya wadda ta gaza yaki da annobar”, “kasar ta farko a duniya wadda take fama da takkadamar siyasa”. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan