Siyasantar da batun cutar COVID-19 zai haifar da illa ga daukacin dan Adam
2021-08-09 15:19:47 CMG
Zuwa yanzu, mutane fiye da miliyan 200 a fadin duniya sun harbu da cutar COVID-19, a yayin da cutar ta halaka wasu fiye da miliyan 4 da dubu 250. Kamar wasu cututtuka masu matukar yaduwa irinsu cutar Plague da aka samu da beraye, da murar Sifaniya, cutar COVID-19 ita ma daya ce daga cikin annobar da da ke kawo babbar barazana ga daukacin dan Adam. Sai dai ana cikin wani yanayi mafi sarkakiya a wannan karo, domin an siyasantar da batun gano asalin cutar COVID-19, tun lokacin da tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fara kira cutar COVID-19 da “cutar numfashi ta Wuhan”.
Kowa ya san bai kamaka ba a siyasantar da batun binciken asalin cutar COVID-19, domin batun nan ya shafi kimiyya da fasaha, da damar kawar da cutar daga tushenta. Don daidaita wani batu na kimiya da fasaha, ana bukatar a yi taka tsan-tsan, da nuna gaskiya, da sanin ya-kamata. Sai dai maganar siyasa, daidai kamar jita-jitar da wasu ‘yan siyasan kasar Amurka ke yadawa, wai kwayoyin cutar COVID-19 sun fito daga dakin gwajin halittu dake birnin Wuhan na kasar Sin, cike take da karairayi, da zargi maras tushe. Wadannan maganganu ba za su taimaka ga yunkurin binciken asalin cuta ba, illa dai haddasa riciki tsakanin al’ummu da kasashe daban daban. A karshe dai, dan Adam ba za su samu damar gano asalin cutar COVID-19 ba, yayin da karin mutane za su rasa rayukansu sakamakon cutar.
Mun san kasar Amurka tana da karfi a fannin kimiya da fasaha, ya kamata ta nuna sanin ya-kamata game da aikin binciken asalin cutar COVID-19. Kana bisa matsayinta na kasar da ta samu mafi yawan mutanen da suka kamu da cutar, da wadanda suka rasu sakamakon cutar(zuwa ranar 8 ga wata, wasu mutane fiye da miliyan 35.75 na kasar suka kamu da cutar COVID-19, yayin da yawan mutanen da suka rasa rayuka ya zarce dubu 616), ya kamata kasar Amurka ta yi kokarin samar da gudunmowa ga kokarin kawo karshen annobar. Sai dai a ganin ‘yan siyasan kasar Amurka, moriyar da ake iya samu yanzu ta fi muhimmanci, inda suke fakewa da jita-jitar cewa kasar Sin ta haddasa bazuwar cutar COVID-19, don boye laifinsu na kasa daukar matakai masu kyau wajen dakile cutar, ta yadda ba za su rasa goyon baya daga jama’ar kasarsu ba. Saboda haka, wadannan ‘yan siyasan kasar Amurka, da kafofin yada labaru na kasar, sun yi kokarin yayata maganar wai cutar COVID-19 ta bazu daga cikin dakin gwajin halittu na Wuhan, kana sakateriyar hukumar lafiya ta duniya WHO, bisa matsin lambar da kasar Amurka ta yi mata, ta gabatar da shirin sake kaddamar da binciken asalin cutar COVID-19 a birnin Wuhan na kasar Sin.
Game da yunkurin siyasantar da batun binciken asalin cutar COVID-19, musamman ma binciken da ake son gudanar da shi a birnin Wuhan don dora wa kasar Sin laifi, kasar Sin sam ba ta yarda ba. Kowa ya sani, a watan Janairu da na Fabrairun bana, kwararru na hukumar WHO sun riga sun kammala wani bincike a birnin Wuhan, kana sun gabatar da sakamakon binciken cewa ba zai yiwu ba a samu asalin kwayar cutar COVID-19 daga dakin gwajin halittu dake Wuhan. To, tun da an riga an yi bincike tare da samun sakamako, me ya sa ake bukatar sake yin wani bincike a Wuhan? Kawai domin neman samar da wani sakamakon da zai gamsar da kasar Amurka? A shekarar 2003, kasar Amurka ta taba yin amfani da garin wanke tufafi a matsayin “shaida” don zargin kasar Iraki da mallakar makamai masu kare dangi. Kasar Sin ba za ta yarda da sake abkuwar irin wannan batu ba.
Hakika akwai wurare daban daban a duniyarmu dake bukatar a gudanar da binciken gano asalin cutar COVID-19. A kasar Amurka kadai ana samun batun rufe cibiyar gwajin halittu na Fort Detrick ba zato ba tsammani, da bullar cutar numfashi da ba a san mece ce ita ba a jihar Virginia, da dai sauransu, duk a shekarar 2019, wadanda dukkansu na janyo shakku sosai. Saboda haka, zai fi dacewa a gudanar da binciken asalin cutar COVID-19 a kasar Amurka da sauran wurare, maimakon sake gudanar da wani bincike a birnin Wuhan na kasar Sin.
Jama’ar duniya sun san wane ne mai adalci. A ranar 2 ga watan Agusta, wasu jam’iyyu da kungiyoyin al’umma, da na masana, fiye da 300, na wasu kasashe da yankuna fiye da 100, sun mika wata hadaddiyar sanarwa ga sakateriyar hukumar WHO, inda suka jaddada cewa, ana bukatar karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban don tinkarar cutar COVID-19, don haka ya kamata a gudanar da binciken asalin cutar COVID-19 cikin adalci da gaskiya, maimakon siyasantar da batun.
Ke nan jama’ar kasashe daban daban sun riga sun bayyana ra’ayinsu, idan wasu ‘yan siyasan kasar Amurka na son ci gaba da daukar matakai na kuskure, to, suke da alhakin tsanantar yanayin cutar COVID-19, da laifin haddasa hasarorin rayukan dubun-dubatar jama’a. (Bello Wang)