Gasar tseren agwagin roba
2021-08-10 16:18:20 CRI
Gasar tseren agwagin roba da aka shirya a jihar Illinois dake kasar Amurka don tallafa wa jama’a. An sanya agwagin dubu 70 a cikin kogi, idan ake biyan dala biyar ga duk agwagwa daya. Wanda agwagwarsa ta yi nasara a gasar zai samu kyautar mota. An dai shirya bai wa kwamitin kula da gasar wasannin Olympics ta nakasassu na jihar Illinois dukkan kudaden da aka tara.