logo

HAUSA

Kudurin Amurka game da taimakawa Taiwan na samun iznin ‘yar kallo a babban taron kiwon lafiya na duniya ba shi da ma’ana

2021-07-30 21:18:12 CRI

Kudurin Amurka game da taimakawa Taiwan na samun iznin ‘yar kallo a babban taron kiwon lafiya na duniya ba shi da ma’ana_fororder_730

Kwanan baya kwamitin huldar kasashen waje na majalisar dattijai ta kasar Amurka ya zartas da wani kudurin dake shafar yankin Taiwan na kasar Sin, inda ya nemi majalisar gudanarwar kasar da ta tsara wani tsari domin taimakawa Taiwan da ya sake samun iznin kasancewa ‘yar kallo a babban taron kiwon lafiya na duniya, Wannan wani sabon mataki ne da wasu ‘yan siyasar Amurka suka dauka domin tsoma baki a cikin harkokin gidan kasar Sin, matakin da ya sabawa ka’idojin sanarwowi uku da kasashen biyu wato Sin da Amurka suka sa hannu, kana ya sabawa dokar kasa da kasa da ka’idar huldar kasa da kasa, a don haka kasar Sin ta nuna adawa da shi da kakkausar murya.

Tun daga shekarar 2009, zuwa 2016, yankin Taiwan na kasar Sin ya taba halartar babban taron kiwon lafiya na duniya da sunan “Taipei na al’ummun kasar Sin” a matsayin ‘yan kallo, an kuma amince da lamarin ne bisa tushen ka’idar “kasar Sin daya kacal a duniya” bayan tattaunawa da aka yi, amma tun bayan da jam’iyyar ci gaban demokuradiyya ta Taiwan ta kama mulki a yankin, ta ki amincewa da ka’idar “kasar Sin daya kacal a duniya”, inda take kokarin neman samun ‘yancin kan Taiwan, a sanadin haka ba zai yiwu a baiwa yankin Taiwan damar halartar babban taron kiwon lafiya na duniya.

Hakika tun daga shekarar 2017, babban taron kiwon lafiya na duniya ya rika kin amincewa da shigar da kudurin “gayyatar yankin Taiwan na halartar babban taron kiwon lafiya na duniya a matsayin ‘yar kallo” a batutuwan da za a tattauna yayin taron, lamarin da ya nuna cewa, ka’idar “kasar Sin daya kacal a duniya” ta riga ta samu amincewa daga al’ummun kasa da kasa, a don haka, bai zai yiyu a kawo mata barazana ba.(Jamila)