logo

HAUSA

Kasar Sin ta nanata adawarta da halartar yankin Taiwan babban taron hukumar lafiya ta duniya

2021-05-21 19:46:59 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, kasarsa ba ta zata lamunci yankin Taiwan ya halarci babban taron hukumar lafiya ta duniya (WHA) ba, a wani mataki na kare ‘yanci da cikakkun yankunanta.

Zhao ya bayyana haka ne Juma’ar nan, yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, gabanin babban taron na WHA karo na 74, da zai gudana ta kafar bidiyo daga ranar 24 ga watan Mayu zuwa 1 ga watan Yuni. Yana mai cewa, hukumomin yankin Taiwan ba su samu gayyata daga hukumar lafiya ta duniya (WHO) na halartar zaman ba. Shi dai babban zaman na WHA, nan ne ake yanke duk wata shawara game da batutuwan da suka shafi WHO.

Zhao Lijian ya bayyana cewa, kasar Sin dai daya ce tak a duniya, kuma gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin (PRC) ita ce halastacciyar gwamnati dake wakiltar kasar Sin baki daya, kuma yankin Taiwan, wani bangare ne na kasar Sin da ba za a yi raba shi ba.

Ya jaddada cewa, wajibi ne duk wasu ayyukan hukumomin kasa da kasa da yankin na Taiwan zai halarta, ciki har da WHO, su dace da manufar “kasar Sin daya tak a duniya”. Yana mai cewa, wannan manufa ta samu amincewar kudirin babban taron MDD mai lamba 2758 da kudiri na 25.1 na babban taron hukumar lafiya ta duniya (WHA). (Ibrahim)

Ibrahim