logo

HAUSA

Majalisar kiwon lafiyar duniya ta yi watsi da batun dake shafar Taiwan

2021-05-25 10:39:34 CRI

Majalisar kiwon lafiyar duniya ta yi watsi da batun dake shafar Taiwan_fororder_Taiwan

Majalisar kiwon lafiya ta duniya WHA, wacce ita ce majalisar koli ta hukumar lafiya ta duniya WHO, a jiya Litinin ta ki amincewa da shigar da batun dake shafar Taiwan cikin ajandun da za ta tafka mahawara kansu.

Chen Xu, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa wakilan kasar Sin sun nuna cikakken goyon bayansu ga matakin da babban taron kwamitin majalisar kiwon lafiyar duniyar WHA karo na 74 ya dauka na kin shigar da batun dake shafar Taiwan cikin ajandunsa.

Chen ya ce, Taiwan bangare ne na kasar Sin wanda ba za a taba raba shi ba, kudiri mai lamba 2758 na babban taron MDD wato UNGA da kuma kudirin majalisar lafiyar WHA mai lamba 25.1 sun samar da dokoki ga WHO da ta mutunta manufar kasar Sin daya tak a duniya, kana da amincewa da Taiwan a matsayin wani bangaren kasar Sin. Duk wani yunkuri na gabatar da batun dake shafar Taiwan ya saba manufofi da kuma take yarjejeniyar MDD, kuma ya saba da kundin tsarin hukumar WHO da dokokin majalisar lafiyar WHA, kuma haramtacce ne marar tushe.(Ahmad)