logo

HAUSA

Yaushe Ne ‘Yan Siyasan Amurka Za Su Daina Goyon Bayan Taiwan Ta Halarci Babban Taron WHO?

2021-05-20 21:18:24 CRI

Nan ba da dadewa ba ne za a bude babban taron hukumar kiwon lafiyar kasa da kasa wato WHO karo na 74. Tsirarrun kasashen yammacin duniya sun sake ambaton batun Taiwan. Kwanan baya, Antony Blinken, sakataren harkokin wajen Amurka ya ce, kin yarda da yankin Taiwan ya halarci taron, zai kawo cikas ga cimma manufar kiwon lafiyar duniya. Haka kuma taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G7 ya ba da wata sanarwar hadin gwiwa, inda ya ambato batun goyon bayan Taiwan ya halarci babban taron WHO.

Kamar yadda WHO ta yi a baya, a bana ta sake kin yarda da gayyatar yankin Taiwan ya halarci babban taron. Wannan shi ne karo na 5 a jere da ta ki amincewa yankin Taiwan ya halarci babban taron tun shekarar 2017. Amurka da tsirarrun kasashen yammacin duniya sun kasa cimma burinsu.

Ko ta yaya ba za su cimma burin ganin yankin Taiwan ya halarci babban taron WHO ba. Wannan na nuna cewa, hakan ya saba wa “ka’idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya” da kuma ra’ayi daya da kasashen duniya suka cimma.

‘Yan siyasan Amurka sun san da haka sosai. Amma ba su so yin watsi da duk wata damar da ke gabansu wajen hana ci gaban kasar Sin. Hakika a karkashin ka’idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, babban yankin kasar Sin ya amince da Taiwan ya shiga ayyukan kiwon lafiyar kasa da kasa yadda ya kamata. Alkaluma sun nuna cewa, tun bayan shekarar 2020, kwararru masu ilmin fasahar likitanci na Taiwan sun halarci harkokin WHO har sau 16. Bayan haka kuma, Taiwan da WHO suna tuntubar juna yadda ya kamata, ta yadda Taiwan ya samu isassun muhimman bayanan da suka shafi rigakafin COVID-19 a kan lokaci. Ya kuma shiga shirin COVAX kamar yadda yake bukata. Don haka bayanan da Amurka ta yi wai babban yankin kasar Sin ya kawo wa Taiwan cikas wajen yaki da annobar ta COVID-19, surutun banza ne kawai.

Kamar yadda Amurka da wasu tsirarrun kasashe suka yi a baya, a bana sun sake yi wasan siyasa bisa hujjar batun Taiwan, a yunkurin hana ci gaban kasar Sin. Tabbas a karshe ba za su cimma burinsu ba kamar yadda suka yi a baya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan