logo

HAUSA

‘Yan wasan alkahura na kasar Sin sun cimma babbar nasara a gasar Olympics ta Tokyo

2021-08-07 20:45:19 CRI

‘Yan wasan alkahura na kasar Sin sun cimma babbar nasara a gasar Olympics ta Tokyo_fororder_d009b3de9c82d1588fbf62d8ebe0f5d0bd3e4288

A wasan karshe na gasar alkahura cikin ruwa na maza na tsayin mita 10 da aka yi a yau Asabar a wajen gasar Olympics dake gudana a birnin Tokyo na kasar Japan, dan wasan kasar Sin Cao Yuan ya samu lambar yabo ta zinari, al’amarin da ya sa kawo yanzu ‘yan wasannin kasar Sin suka samu lambobin yabo na zinari guda 38 a wajen Olympics na bana. Dan wasan kasar na daban Yang Jian ya samu lambar yabo ta azurfa.

‘Yan wasan gasar alkahura cikin ruwa na kasar Sin sun kammala dukkan gasanninsu 8, inda suka samu lambobin yabo na zinari 7 tare da na azurfa 5. (Murtala Zhang)