logo

HAUSA

Shirye shirye gasar Olympics ta hunturu ya ingiza matakin tallafawa nakasassu

2021-08-05 13:58:51 CRI

Shirye shirye gasar Olympics ta hunturu ya ingiza matakin tallafawa nakasassu_fororder_src=http___a3.peoplecdn.cn_1a65ca82349d17b7221f6c834f4dade0&refer=http___a3.peoplecdn

A ranar 9 ga watan Yulin nan ne aka kaddamar da karo na 2, na aikin dudduba wuraren gudanar da wasanni marasa shinge da za a yi amfani da su, yayin gasar Olympics ta lokacin hunturu dake tafe badi a birnin Beijing. Kwararru a fannin duba irin wadannan filaye, da kayayyakin wasa na kwamitin gasar nakasassu ta lokacin hunturu, da sauran sassan masu ruwa da tsaki ne suka dudduba wuraren 12, da kauyuka wasan 3  masu nasaba da wuraren gasanni 3.

Game da hakan, daraktan tsare tsare na wuraren gudanar da wasanni ajin nakasassu, a kwamitin shirya gasar ta Olympics ta Beijing Peng Sitian, ya ce aikin dudduba wurare da kayayyakin gudanar da gasar ajin nakasassu, na da nufin fayyace matsayin ayyukan gine ginen wuraren gasa, da kauyukan gasa a matakin farko na tabbatar da ingancin wuraren da ba su da shinge, tare da duddubawa, da kawar da matsalolin da aka taras don tabbatar da ingancin su. Domin bukatar tabbatar da ingancin wadannan wurare, batu ne da ya shafi kowa da kowa.

Manema labarai da suka halarci babban filin wasa na kasa sun ganewa idanun su, yadda aka yiwa babban filin wasa na kasar Sin gyaran fuska, gabanin gasar dake tafe a shekara mai zuwa, inda ake sa ran gudanar da gasar hunturu ta wasan gora na kankara ko “Ice hockey” ajin maza da mata, da ajin gasar na nakasassu.

Domin cimma bukatun gasar, an gudanar da gyare gyare da dama ga sassan da za a gudanar da gasar, wadda ke bukatar filaye marasa shinge. Ga misali, an tsara na’urorin hawa sama, ta yadda za su zama ba bu shinge, domin jin dadin nakasassu, ta yadda za su iya isa ga wuraren gudanar da gasar ta kofofi daban daban ba tare da wata matsala ba.

Wani karin misalin shi ne, wuraren zama marasa kariya, wadanda aka sanya a wurare da dama a filayen wasan, domin baiwa ‘yan kallo masu nakasa damar kusantar wurin da za a buga kwallon gora. A yayin gasar ajin nakasassu, tun daga wurin adana kayayyakin ‘yan wasa har zuwa filin buga wasa, an rage santsin daben wuraren, ta yadda masu nakasa za su samu saukin bi, ba tare da wata wahala ba. Kaza lika ‘yan wasa za su iya gangarawa zuwa wurin ajiyar kayayyakin su daga dukkanin sassa.

Tawagar hadin gwiwar masu sa idon sun shiga filin wasan na kasa, sun yi safiyon wuraren wasa marasa shinge, da bandakuna, da wuraren sauya tufafi, da sauran wurare marasa shinge, kafin hada cikakken bayanin yanayin su.

Zhao Lin, kwararre ne a fannin lura da wuraren wasa marasa shinge, wanda kuma ya kasance cikin tawagar masu nazarin, kuma babban injiniya ne a cibiyar masu zane-zanen gine gine da bincike ta kasar Sin, ya bayyana muhimmancin wadannan irin filaye da yadda tasirin su zai shafi kowa da kowa.

Zhao Lin ya ce "Bayan ko wane dan wasa ko dan kallo ya shiga fili, za a samu damar nuna dukkanin faya fayen da ake bukata kan allon bidiyo yadda ya kamar. Daga daidaikun wurare, zuwa layukan kasa, dole a maida hankali ga bukatun sassa daban daban, musamman cikakkun bayanai game da kayan bukata da na wasa. Lokacin duba wuraren da na kammala ba jimawa ba, na maida hankali sosai ga duba muhimman abubuwan bukatu, na wurin hutawar ‘yan wasa, da bandakuna, da sauran  kayayyaki da ake matukar bukata, kamar kofofin shigar ‘yan wasa da marikin gefen bene. Kusan ma dai, irin wadannan kayayyakin ba masu bukatar musamman ne kadai ke bukatar su ba. Mutane ake tanadarwa wadannan abubuwan hidima da kula. Don haka, ko a wasannin hunturu ko na zafi ajin nakasassu, akwai irin wadannan kayayyaki da ko da yaushe ana bukatar su, domin amfanin su ga mutane."

Kara yayata manufar tallafawa nakasassu

Ta hanyar shirya gasar Olympics ta birnin Beijing da gasar ajin nakasassu, ana iya kara inganta yanayin wuraren wasa marasa shinge da gina al’ummar bai daya.

An amince cewa, wannan aiki ya shafe kusan shekaru sama da 5 ana aiwatar da shi. Gwamnatocin biranen Beijing da Zhangjiakou, bisa dogaro ga wannan gasa ta lokacin hunturu, sun tsara manufofin gina wadannan nau’oin filayen wasa, da suka hada hanyoyin birane, da tsarin sifiri, da hidimomin al’umma. Har ila yau musayar bayanai, ta samar da karin dama ta yayata gina yanayi mai kyau maras shinge, da gaggauta inganta matsayin sassan wadannan ayyuka.

A yanzu haka, kayayyakin wasan marasa shinge da za a yi amfani da su a sassan gasar, na samun gyare gyare, ana kuma kara daga matsayin su. A birnin Beijing, dukkanin yankunan dake da gargada, da tituna da suke da matsala an gyara mafi yawan su, an kuma tsara hanyoyin sufuri marasa shinge yadda ya kamata. Har ila yau, an gudanar da aiki na musamman, don kyautata yanayin karuwa ko raguwar zafi a yankunan birnin.

A birnin Zhangjiakou ma, gundumomi daban daban sun fara gudanar da ayyukan kyautata wuraren wasa marasa shinge, yayin da suke kara karfafa ayyukan kyautata tituna, da kwanoni, da na’urorin hawa sama, da ban dakuna, da wuraren ajiya ababen hawa, da allunan nuna wurare, da da kananan abubuwan bukata a masaukan baki da wuraren jira, domin samar da kyakkyawan yanayi ga masu bukata ta musamman, ta yadda za su shiga a dama da su, su kuma samu saukin gudanar da dukkanin ayyukan zamantakewa.

Manyan wuraren gudanar da gasar marasa shinge dake wuraren gudanar da gasar ta lokacin hunturu ta Beijing, da ta ajin nakasassu, ba kawai za su biya bukatun al’umma ba ne bayan kammalar gasar, har ma za su zamo wani mizani ne na auna ayyukan da za a yi nan gaba a wannan fanni.

Da take tsokaci kan hakan, mataimakiyar shugaban gungun kungiyoyin masu bukata ta musamman na kasar Sin Wang Meimei, ta ce karbar bakuncin gasar Olympics ta birnin Beijing da ta ajin nakasassu, zai yi matukar tasiri ga ayyukan yayata ci gaban zamantakewa, da ingiza ginin al’umma mai makomar bai daya. Ta ce "A shekarun baya bayan nan, Sin ta cimma matsayar kariyar shari’a, da moriyar masu bukata ta musamman, tare da inganta yanayin rayuwar su baki daya a dukkanin fannoni".

Jami’ar ta kara da cewa "Yanzu haka ‘yan na’urori kalilan masu bukatar musamman ke bukata. Da kuma abubuwa marasa shinge, domin yin rayuwa mai sauki da jin dadi. Ga misali, masu bukatar musamman na iya amfani da kujerar guragu, da sandunan taimakawa tafiya, da na’urar taimakawa marasa kafa hawa sama, da na’urar hawa sama maras shinge, da nau’in motocin bas masu saukin hawa gare su, ta yadda su ma za su ji dadin rayuwa.

A daya bangaren kuma, masu matsalar gani na iya cimma nasarar rayuwa mai nagarta, ta hanyar karanta bayanai ta amfani da rubutun da ake karantawa da yatsu da manyan haruffa, ta yadda za su iya karanta litattafai kamar kowa. Har ma su rika shiga yanar gizo dake gabatar da bayanai ta haruffan da ake karantawa da hannu.

Har ila yau, masu larurar ji, su ma za su iya zantawa da masu ji ta hanyar yaren su da suke koya, da ta amfani da na’urorin tallafawa ji, da horon sauraron yaren kurame. Yayin da ake kara inganta kayayyakin amfanin  yau da kullum marasa shinge, hakan na kara inganta rayuwar masu bukatar musamman, ta yadda za su kara shiga harkokin zamantakewar al’umma a dama da su yadda ya kamata.