logo

HAUSA

‘Yan wasan tseren Ghana 4 sun bayyana gamsuwa da kwazon su a gasar Olympics

2021-08-09 10:30:59 CRI

‘Yan wasan tseren Ghana 4 sun bayyana gamsuwa da kwazon su a gasar Olympics_fororder_微信图片_20210809103016

‘Yan wasan tseren karba karba na kasar Ghana Sean Safo-Antwi, da Benjamin Azamati, da Emmanuel Yeboah, da kuma Joseph Paul Amoah, sun bayyana gamsuwa da irin rawar da suka taka yayin gasar Olympics ta birnin Tokyon kasar Japan.

Da yake tsokaci kan hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, kyaftin din ‘yan wasan da suka fafata a gudun mita 100 ajin ‘yan wasa 4 Joseph Paul Amoah, ya ce duk da dakatar da su da aka yi yayin gasar da suka shiga saboda saba ka’idar wasa, a hannu guda sun yi farin ciki da kwazon da suka nuna, kuma nan gaba za su kara kyautata kwarewar su.

Joseph Paul Amoah, ya ce za su koma su duba kura kuran su domin yin gyara, kuma za su fuskanci gasar kasa da kasa da za a gudanar a Oregon, wadda tuni suka samu gurbin shiga, inda suke fatan nuna bajimtar su yadda ya kamata.  (Saminu)