logo

HAUSA

Yadda masu ciki suke motsa jiki kullum yana kyautata jikin ‘yan tayi

2021-08-08 19:23:22 CRI

Yadda masu ciki suke motsa jiki kullum yana kyautata jikin ‘yan tayi_fororder_src=http___ci.xiaohongshu.com_44a0befe-24a6-4494-8126-7f96666bff7e@r_750w_750h_ss1&refer=http___ci.xiaohongshu

Wani nazari mai ban sha’awa da aka gudanar ya nuna mana cewa, idan masu ciki suna motsa jiki kullum, to, akwai yiwuwar jariran da suke dauke da su, za su fi sauran takwarorinsu saurin girma a fannin daidaituwar jiki. Wannan nazari ya sake shaida cewa, motsa jiki a lokacin da aka samu ciki, yana amfana wa masu juna biyu, haka kuma yana kyautata lafiyar ‘yan tayi, da yin tasiri kan kwarewarsu ta motsa jiki a nan gaba.

Gwamnatocin kasashen Amurka da Turai sun ba da shawarar cewa, kamata ya yi kananan yara su ware a kalla awa daya suna gudu suna wasa a kowace rana. Amma sulusin kananan yara da ke zama a Amurka da Turai suna motsa jiki kamar yadda aka shawarta. Akwai dalilai da dama da suka sa haka, alal misali, ba sa motsa jiki isasshe a makaranta, suna fama da matsalar kiba. Amma masu nazari daga Amurka sun yi tunanin cewa, ko yanayin da masu juna biyu suke kasancewa zai yi tasiri, wanda ba a taba zato ba a baya?

Masu nazarin daga jami’ar East Carolina ta Amurka sun gudanar da nazari kan ko motsa jiki a lokacin samun ciki zai yi tasiri kan kwarewar daidaituwar jikin jarirai ko a’a.

Masu nazarin sun gayyaci masu juna biyu 71 masu koshin lafiya, wadanda yawancinsu suke cikin watanni 3 na farkon lokacin samun ciki, kuma suna da ‘yar tayi ko dan tayi daya tilo a cikinsu. Wadannan masu aikin sa kai an raba su cikin rukunoni 2 da ka. Masu juna biyu cikin rukuni na A sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum. Masu juna biyu cikin rukuni na B kuma sun fara motsa jiki, suna saduwa da masu nazarin sau 3 a kowane mako. Bisa shawarar masu nazarin, sun dauki mintuna 50 suna motsa jiki, ta hanyoyin yin gudu sannu sannu, yin tafiya cikin sauri, hawan keken motsa jiki da rawar motsa jiki. Sun yi ta motsa jiki har kafin su haihu.

Bayan wata guda da aka haifi jariran, wani likitan kula da kananan yara ya yi bincike kan jariran, dangane da yadda wadannan jarirai suke sarrafa kawunansu yayin da suke kwance a gado, yadda suke iya dunkule hannu, mirginawa, mike hannu da dai sauransu.

Sakamakon binciken ya dace da hasashen da aka yi a baya. Idan mahaifan jariran mata da suka rika motsa jiki yayin da suke dauke da ciki, to, jariransu sun fi yin fintikau cikin binciken kusan a dukkan fannoni., lamarin da ya nuna cewa, sun fi nuna kwarewar motsa jiki.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, idan kananan yara sun fi takwarorinsu iya motsa jiki, to, an karfafa musu gwiwar kara motsa jiki, haka kuma bayan da suka girma, sun fi sha’awar motsa jiki cikin himma da kwazo.  (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan