logo

HAUSA

Kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashe makwabta zai samar da ci gaba da zaman lafiyar da duniya ke bukata

2021-08-03 16:26:21 CRI

Kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashe makwabta zai samar da ci gaba da zaman lafiyar da duniya ke bukata_fororder_微信图片_20210803162155

Shugabannin kasashen Tanzaniya da Rwanda sun rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin da suka shafi ayyukan more rayuwa da nufin inganta rayuwar jama’arsu da samun moriyar juna.

Tanzaniya da Rwanda sun kasance kasashen nahiyar Afrika daga yankin gabashin nahiyar, haka kuma makwabtan juna dake da al’adu da harshe masu kamanceceniya da juna. Yayin da ake kira da dunkulewar nahiyar Afrika da ma duniya baki daya, har ma da inganta huldar kasa da kasa, za a iya ganin matakin da wadannan kasashe makwabta suka dauka a matsayin wanda ya dace a lokacin da ya dace.

Daga cikin yarjejeniyoyin da suka rattabawa hannu akwai ta shimfida layin dogo, wanda zai kasance muhimmiyar alama ta dangantakar kasashen biyu. Haka kuma zai bude kofa ga fadada yarjejeniyoyi da dama a tsakaninsu, wadanda za su kai su ga samun ci gaba da kuma amfanawa al’ummominsu. Har ila yau, zai bunkasa dangantakar cinikayya dake tsakaninsu, sannan ya karawa ’yan kasuwa kuzari da saukaka zirga-zirga. Bugu da kari zai samar da karin karfi ga masana’antu wajen kara yawa da ingancin kayayyaki, da samar da karin guraben ayyukan yi ga jama’arsu, har ma da amfana daga albarkatun da suka mallaka.

Wani bangare na yarjejeniyar ya shafi batun shige da fice. Ko ba komai, ya kamata a ce a saukaka matakan shige da fice a tsakaninsu domin bunkasa musaya da hulda da zamantakewa tsakanin al’ummomin kasashen da kawar da duk wata tangarda da jigilar kayayyaki tsakanin iyakoki ke fuskanta. Kamata ya yi a ce ana samun irin wannan hadin gwiwa tsakanin kasashe makwabta, domin samun ci gaban da ya dace a tsakaninsu, har ma da ba sauran kasashen waje kwarin gwiwar hada hannu da su wajen gudanar da ayyukan moriyar juna. Baya ga haka, zai tabbatar da fahimta da zaman lafiyar da duniya ke matukar bukuta. Domin kyakkawar dangantaka tsakanin gwamnatoci da al’ummomin kasashe makwabta, zai sa su dogara da juna, inda za su fi mayar da hankali wajen kyautata dangantakarsu da alfanun da suke samu maimakon rikici da tashin hankali. (Faeza Mustapha)