logo

HAUSA

Sojojin kasar Sin sun samar da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya

2021-08-01 16:56:10 CRI

Ranar 1 ga watan Agusta, rana ce da aka kafa rundunar sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin. A shekarun baya-baya nan, rundunar sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin ta zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu da sauran sojojin kasa da kasa, da samar wa kasashen duniya kayayyakin kiyaye zaman lafiya, ta yadda ta shaida mutuncin Sin na babbar kasa mai sauke alhakin dake wuyanta, da kuma samar da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da na karko a duniya.

A shekarun baya-baya nan, rundunar sojojin kasar Sin ta kara nuna goyon baya ga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD. Ta kuma kara kawo imani da kyakkyawan fata ga aikin sa kaimi ga warware rikice-rikice, da kiyaye zaman lafiya a yankuna, da samun ci gaba cikin lumana.

Kasar Mali dake yammacin Afirka yanki daya ne dake cikin yankuna mafi hadari da MDD ke gudanar da ayyuka. Amma wannan bai tsorata sojojin Sin ba, inda sojojin kasar 413 na rundunar kiyaye zaman lafiya karo na 8 dake kasar Mali, suka kammala ayyukansu na tabbatar da tsaro, da yin sintiri, da aikin gine-gine, da samar da jinya da sauran ayyuka cikin nasara, don haka suka samu lambar yabo ta kiyaye zaman lafiya ta MDD. Sojojin Sin ba sa jin tsoron tinkarar kalubale daban daban bisa yanayinsu da kwarewarsu, don shaida matsayin Sin na babbar kasa mai sauke nauyin dake wuyanta. (Zainab)