Sama da jami’an lafiya 500 Sin ta aike Saliyo tun daga shekarar 1973
2021-07-30 09:37:47 CRI
Jakadan Sin a Saliyo Hu Zhangliang ya ce daga shekarar 1973 zuwa yanzu, Sin ta tura jami’an lafiya sama da 500 zuwa Saliyo, domin taimakawa kasar dake yammacin Afirka da hidimomin kiwon lafiya da na jinya.
Jakada Hu Zhangliang ya bayyana hakan ne ta kafar bidiyo a jiya Alhamis, albarkacin bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Saliyo, wanda aka gudanar daga birnin Freetown fadar mulkin Saliyo.
Jakadan ya kara da cewa, cikin shekaru 50 da suka gabata, sassan biyu sun fadada hadin gwiwar su ta fuskar hada hadar cinikayya, da raya tattalin arziki.
A nasa tsokacin kuwa, ministan ma’aikatar harkokin wajen Saliyo David Francis, jinjinawa kasar Sin ya yi, bisa ayyukan raya kasa da ta shafe tsawon wadannan shekaru tana aiwatarwa a Saliyo, matakin da a cewar sa ya samar wa kasar moriya mai yawa.
Ministan ya kuma jaddada aniyar Saliyo ta ci gaba da ingiza kawancen sassan biyu zuwa mataki na gaba. (Saminu)