logo

HAUSA

Ese Brume ta samu lambar tagulla a wasan tsallen badake na mata

2021-08-04 10:25:11 CRI

Ese Brume ta samu lambar tagulla a wasan tsallen badake na mata_fororder_i

Zakarar duniya Malaika Mihambo ta yunkura a damarta ta karshe ta lashe lambar Zinare a gasar tsallen badake ta mata. ‘Yan wasa Brittney Reese daga Amurka da Ese Brume ta Nijeriya ne suka kankane matakin karshe na gasar. Sai dai Mihambo ta yi yunkuri mai karfi na tsallen mitoci 7 a tsallenta na karshe yayin wasannin Olympics na Tokyo da aka yi jiya Talata.

Brittney Reese da Ese Brume sun samu dama, sai dai cikinsu babu wadda ta yi tsalle mai nisa.

Dukkansu biyu sun tsaya ne a mita 6.97, sai dai Brittney Reese ta samu lashe lambar Azurfa yayin da Ese Brume ta samu Tagulla. (Fa’iza Mustapha)